Yan bindiga sama da guda 100 sun kai hari garuruwan Neja

Yan bindiga sama da guda 100 sun kai hari garuruwan Neja

Wasu yan bindiga da ake zargin mambobin kungiyar ISWAP ne sun kai hari garuruwan Gurmana, tsohuwar Gurmana da kuma Ashirika da ke karamar hukumar Shiroro a jahar Neja.

Wani idon shaida ya bayyana wa majiyarmu ta Channels TV cewa yan bindiga kimanin su 100 sun kai mamaya garuruwan da misalin karfe 10:00 na safiyar ranar Asabar, 8 ga watan Fabrairu, wasu akan Babura sannan wasu kuma a kafa inda suke ta harbi a sama ba kakkautawa.

Ya cewa harin ya fara ne a Gurmana inda aka rahoto cewar an kashe mutane biyu da raunata wasu hudu kafin su koma tsohuwar Gurmana inda suka yi fashin shanu sama da guda 200.

A halin da ake ciki, a daidai lokacin kawo wannan rahoton, yan sanda basu rigada sun tabbatar da hare-haren da yawan mutanen da aka kashe a garuruwan ba. Amma sanata mai wakiltan Neja ta gabas, Sani Musa ya tabbatar da samun rahotannin hare-haren a safiyar ranar Asabar.

Yan bindiga sama da guda 100 sun kai hari garuruwan Neja
Yan bindiga sama da guda 100 sun kai hari garuruwan Neja
Asali: Twitter

"Zuciyana ya yi nauyi, kuma na kasa yarda cewa mutane za su iya kasancewa da rashin tsoron Allah har ya kai ga rayukan jama’a ya zama ba komai ba a wajensu. Na samu rahoton abun bakin cikin da kuma hare-haren rashin imani da aka kai kan mutane na a safiyan nan.

“A bisa ga bayanin da na samu, yan bindiga sanye da bakaken kaya da rufaffen fuskoki sun kai mamaya garin Gurmana da wasu garuruwa sannan suka fara harbi ba kakkautawa. A cikin haka mutane biyu sun mutu yayinda hudu ke kwance a asibiti cikin mawuyacin hali,” in ji shi.

Dan majalisar, yayinda yake yaba ma jami’an tsaro a sabon kokarin da suke yin a magance rashin tsaro a jihar, ya bukaci da kada su yi kasa a gwiwa.

KU KARANTA KUMA: Babu abinda zan iya yi kan karin harajin katin kiran waya – Pantami

“Ina kira ga dukkanin hukumomin tsaro a jahar, musamman dakarun da ke aiki a yankunan Shiroro, Munya, Rafi, Paikoro da Mashegu da sauran yankuna a kokarinsu na magance annobar rashin tsaro a jihar. Ya zama dole na kara da cewa, na yaba kokarinsu sosai,” in ji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel