Minista ya yi murabus saboda dukan mace mai gadi a kasar waje

Minista ya yi murabus saboda dukan mace mai gadi a kasar waje

- Ministan shari’a na Rwanda, Evode Uwizeyimana ya ajiye aikinsa bayan ya daki wata mai aikin gadi inda ta fadi kasa

- Sai dai kuma Mista Uwizeyimana ya nemi afkuwa a shafin Twitter, inda ya nuna nadama kan abun da ya afku

- Daga bisani Ministan ya ziyarci matar wacce ke gadi a ofishin da take aiki

Rahotanni da muke samu sun nuna cewa ministan shari’a na Rwanda, Evode Uwizeyimana ya ajiye aikinsa bayan ya daki wata mai aikin gadi inda ta fadi kasa.

Shafin BBC ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a ranar Litinin.

An kuma tattaro cewa lamarin ya bazu ne bayan da wani da ya shaidi afkuwar lamarin ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Sai dai kuma Mista Uwizeyimana ya nemi afkuwa a shafin Twitter, inda ya nuna nadama kan abun da ya afku.

Minista ya yi murabus saboda dukan mace mai gadi a kasar waje
Minista ya yi murabus saboda dukan mace mai gadi a kasar waje
Asali: Twitter

Ya ce: “ bai kamata a matsayina na shugaba na aikata wannan mummunan abu ba. Ina neman gafarar wannan mata da ke aiki a kamfanin sanar da tsaro sannan kuma Ina neman tafiyar jama’a.”

KU KARANTA KUMA: Masu garkuwa da mutane sun saki yaran wani likitan Kaduna bayan sun kashe mahaifiyarsu

Daga karshe an tattaro cewa ministan ya ziyarci matar wacce ke gadi a ofishin da take aiki.

A wani labarin kuma, mun ji cewa Solomon Peter mai shekaru 23 da ya kashe budurwarshi mai shekaru 25 ya ce ya kasheta ne yayin kare kan shi. Idan zamu tuna, 'yan sanda sun kama Peter ne bayan mutuwar budurwarshi a ranar 24 ga watan Janairu sakamakon sukarta da yayi da wuka a baya.

A yayin tattaunawa da jaridar Daily Trust a ranar Laraba, wanda ake zargin ya ce ya soketa da wuka ne don kare kanshi bayan fadan da suka fara a kan amsa wayar wani gardi da yake zargin saurayinta ne kuma suna cin amanarshi.

Ya ce bayan ta fasa kwalbar a kanshi ne ya shiga daki ya dauko wuka wacce ya soketa da ita, lamarin da yayi sanadin mutuwarta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel