Wani mutum ya fusata Nafisa Abdullahi akan bidiyon Maryam Booth

Wani mutum ya fusata Nafisa Abdullahi akan bidiyon Maryam Booth

Tun bayan bayyanar bidiyon jarumar Kannywood, Maryam Booth a tsirara ne dai mutane ke ta cece-kuce inda abokan aikinta k eta kokarin kareta daga tozarcin mutane musamman makusanta.

A halin haka ne wani matashi da ke amfani da shafin Twitter ya harsala aminiyar Maryam wato Jaruma Nafisa Abdullahi, inda ta kai da har sai da ta zazzage shi ta uwa ta uba.

Nafisa dai ta wallafa a shafinta na Twitter cewa sun san wanda ya saki bidiyon inda ta yi rantsuwar cewa sai mai shi ya yi danasanin aikata hakan.

Tana mai cewa: “Mun san wanda ya aikata hakan kuma Wallahi Wallahi Wallahi, shakka babu sai ya yi danasanin hakan,” fassarar abunda ta wallafa da Turanci.

Wani mutum ya fusata Nafisa Abdullahi akan bidiyon Maryam Booth
Wani mutum ya fusata Nafisa Abdullahi akan bidiyon Maryam Booth
Asali: UGC

A hakan ne matashin mai suna Abdulkadir @abdoolsareeena ya ce ta yi shiru kafin itama a saki nata.

Inda Jaruma Nafisat Abdullahi Ta Wallafa “Ah gidan uwarka za’a releasing nawa? Dan ubanka? Ai Idan akwai masu shi baza su fasa sakewa ba! Meh kama da iblis so I should keep quiet ko? Because Ina tsoron uwarka.

“Bana magana, hayaniya ba abi na bane, amma duk abinda ke yawo akan mutanen zamani nima akwai shi akai na! Ku Sani, kasancewa ta public figure bazai hanani nuna tashanci ba tunda duk yan tasha ne ah nan.... duk mu hadu mu ci mutuncin juna tunda abinda most of you ke so kenan.

“Babu wani abu sabo... ni matsala ta daya ma, lokacin bumshots dinnan ban wani kile ba... Ina ma yanzu ne... da an ga Curves an ga swags.”

KU KARANTA KUMA: Manyan jaruman kannywood sun yi martani kan bidiyon tsiraicin maryam Booth

Ta kara da cewa “But then, I don’t have the energy to be here for long! . . But dika mu Sani!!! Wallahi ah rubuce yake... Duk mutumin da ya tozarta wani Toh Allah Sai ya yi masa abinda yafi abinda yayi!!! Ko ah duniya ko lahira...”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng