Aisha Musa
9376 articles published since 09 Agu 2016
9376 articles published since 09 Agu 2016
Rahotanni sun kawo cewa jami’an tsaro da taimakon wani maharbi sun samo tarin makamai da alburusai wadanda ake zaton na yan fashi ne a dajin Lame-Burra, wani gagarumin maboyar miyagu a jahar Bauchi.
Rahotanni sun kawo cewa gwamnonin da aka zaba a karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na cikin wata ganawa mai muhimmanci a Abuja.
Wata kotun Majistare a jahar Kaduna ta tsare wani Muhammad Isah kan zargin lalata da kananan yaransa mata su biyu. Justis Musa Lawal na kotun Majistare ya kuma dage sauraron shari’an zuwa ranar 30 ga watan Maris 2020.
Wasu yan bindiga da ake zaton masu garkuwa da mutane ne sun sace yaron wani dan kasuwa a Suleja a Chaza, wani gari da ke wajen garin Suleja a jahar Niger.
APC ta dakatar da Kaycee Osamwonyi, hadimin gwamnan jahar Edo, Godwin Obaseki daga jam’iyyar mai mulki kan zargin aikata ta’addanci da kawo rabuwar kai a jam’iyyar mai mulki.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da Injiniya Ahmed Kadi Amshi a matsayin shugaba hukumar da ke kula da majalisar dokokin tarayya, sannan ya kuma kaddamar da wasu 11 a matsayin mambobin hukumar.
An gurfanar da wani matashi dan shekara 16 a gaban kotun majistare na Igbosere da ke jahar Lagas kan zargin boyewa a cikin bayin wani banki tsakar dare sannan ya saci kudi naira 340,000.
Rundunar yan sanda a jahar Niger ta kama wata mata ‘yar shekara 32 wacce aka ambata da suna Hassana Bala kan yunkurin yin garkuwa da wani mutum dan shekara 23, Umar Sarkin Turaku na kauyen Kawo a karamar hukumar Kontagora.
Gwamnan jahar Edo, Mista Godwin Obaseki, ya koka a wajen Shugaban kasa Muhammadu Buhari, cewa Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress na kasa, Adams Oshiomhole da mambobin kungiyar Edo Peoples Movement na so su hargitsa gwamn
Aisha Musa
Samu kari