Yanzun-nan: Gwamnonin PDP sun shiga labule a Abuja
- Gwamnonin da aka zaba a karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na cikin wata ganawa mai muhimmanci a Abuja
- Suna ganawar ne a masaukin gwamnan jahar Sokoto da ke yankin Asokoro, karkashin jagorancin Shugaban kungiyar gwamnonin PDP, Hon. Aminu Waziri Tambuwal
- An gano wasu daga cikin mambobin kwamitin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar ma a wajen taron
Rahotanni sun kawo cewa gwamnonin da aka zaba a karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na cikin wata ganawa mai muhimmanci a Abuja.
Ganawar wanda ya fara yan mintuna kadan da suka gabata na wakana ne a masaukin gwamnan jahar Sokoto da ke yankin Asokoro, karkashin jagorancin Shugaban kungiyar gwamnonin PDP, Hon. Aminu Waziri Tambuwal.

Asali: UGC
Wani hadimin daya daga cikin gwamnonin ya bayyana cewa an kira ganawar ne domin tsayar da magan daya gabannin taron kungiyar gwamnonin Najeriya da za a gudanar a yau Laraba, 26 ga watan Fabrairu, jaridar Tribune ta ruwaito.
A daidai lokacin kawo wannan rahoton an gano wasu daga cikin mambobin kwamitin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a wajen taron.
KU KARANTA KUMA: Yanzu-yanzu: An kai wa shugaban APC na jihar Kwara hari
A wani labari na daban, mun ji cewa Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle ya tarbi kimanin mutane 100,000 da suka sauya sheka daga jam’iyyar APC zuwa jam’iyyarsa a karamar hukumar Zurmi da Shinkafi na Jihar.
A wani jawabi da mai magana da yawun gwamnan, Zailani Bappa, ya rattafa hannu, yace wadanda suka sauya sheka sun koma jam’iyyar PDP ne domin marawa Matawalle baya domin cigaban gwamnatisa.
Wadanda suka sauya shekar sun bayyana cewa sun yanke shawarar komawa PDP ne domin su tabbatar da nasarar da gwamna0n ke samu wajen tabbatar da zaman lafiya da cigaban Jihar.
A jawabansu, shugaban karamar hukumar Zurmi, Auwalu Bawa da tsohon ciyaman din karamar hukumar Shinkafi, Usman Ajiya sun bayyana biyayyar mutane ga gwamnatin Matawalle.
Gwamna Matawalle, a yayin da yake bayyana farin cikinsa kan suaya shekarsu zuwa jami’yyarsa, ya dau alkawarin farantawa kowa rai a Jihar.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng