An Dora Hayatu Deen a gaban Atiku, Obi da Amaechi a Takarar Zama Shugaban Kasa a 2027
- Tsohon mai magana da yawun kwamitin kamfen Atiku Abubakar ya dora manyan jiga-jigan adawa da ke neman takarar shugaban kasa a mizani
- Segun Showunmi ya ce Mohammed Hayatu-Deen shi ne a sahun gaba saboda kwarewarsa da fahimtarsa kan tattalin arziki
- Showunmi ya ce ya kamata ‘yan Najeriya su fara mayar da hankali kan ƙwarewa, manufofi da dabarun shugabanci maimakon hayaniyar siyasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Segun Showunmi ya bayyana daya daga cikin masu neman takarar shugaban ƙasa a ADC, Mohammed Hayatu-Deen, a matsayin mafi karfi a tsakanin 'yan adawa.
Showunmi ya ce Hayatu-Deen ya zarce duk wani dan adawa da ke neman takarar shugaban kasa karfin da zai iya tunkarar shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027.

Source: Twitter
Ya yaba matuka da ƙwarewarsa da fahimtarsa kan tattalin arziki, yana mai cewa shi ya fi dacewa ya karbi mulki, kamar yadda The Nation ta ruwaito.
Showunmi dai ya kasance mai magana da yawun tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, a yaƙin neman zaɓen 2019 da 2023.
An sanya Hayatu-Deen a gaban Atiku
Jigon siyasar ya bayyana hakan ne a wata hira a daren Alhamis yayin da yake nazarin ƙarfin da damar manyan ‘yan adawa gabanin zaɓen 2027.
Ɗan siyasar kuma mai sharhi kan harkokin jama’a ya ce Hayatu-Deen ya bambanta da sauran masu neman takara saboda ƙwarewarsa ta aiki da kuma fahimtarsa kan matsalolin tattalin arzikin Najeriya.
“Shi ne mutumin da yake da mafi kyawun tarihin aiki. Ina ganin ya nuna jarumtaka wajen shiga harkar siyasa domin bayar da gudunmawar gogewarsa wajen yi wa ƙasa hidima,” in ji shi.
Showunmi ya ce ya kamata ‘yan Najeriya su fara mayar da hankali kan ƙwarewa, manufofi da dabarun shugabanci maimakon hayaniyar siyasa da siyasar son rai.
Tsohon mai magana da yawun Atiku, ya ce Najeriya na buƙatar shugabanni masu karfin magance tabarbarewar tattalin arziki tare da dawo da amincewar jama’a ga gwamnati.
Showunmi ya tabo Atiku, Obi da Amaechi
Da yake magana kan damar sauran manyan ‘yan adawa, Showunmi ya amince da gogewa da tarihin siyasar Atiku Abubakar, amma ya nuna cewa ƙasar nan na bukatar shugabanci na zamani.
Game da tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, Showunmi ya ce yana ganin tsohon gwamnan na tafiya ne da burin siyasa da kuma jin cewa ya cancanci shugabanci.

Source: Twitter
Showunmi ya amince cewa tsohon gwamnan Anambra, Peter Obi yana da ƙarfi da magoya baya masu aminci, amma ya jaddada cewa yana bukatar hadin kai daga kowane bangare kafin ya samu nasara.
A karshe, ya nuna cewa Mohammed Hayatu-Deen duk ya sha gaban wadannan manyam jagoroin adawa, yana yabasa da ƙwarewarsa da fahimtarsa kan tattalin arziki.
Atiku da Amaechi sun maida fam din takara
A wani labarin, kun ji cewa manyan jiga-jigan adawa a Najeriya, Atiku Abubakar da Rotimi Amaechi sun maida fam din takara ga jam'iyyar ADC.
Amaechi ya yi alƙawarin gyara Najeriya cikin shekara huɗu idan aka zaɓe shi, yana mai cewa ƙwarewa da ayyukan da mutum ya yi ne ya kamata su ba shi damar takara a 2027.
A nasa bangaren, Atiku ya ce takararsa ta shugaban ƙasa tana wakiltar wani gagarumin yunƙuri na dawo da ci gaba da sake gina Najeriya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

