'Saboda Wasu Ƙasashe ne': Trump Ya Fadi dalilin Tsagaita Wuta da Iran a Yaƙi

'Saboda Wasu Ƙasashe ne': Trump Ya Fadi dalilin Tsagaita Wuta da Iran a Yaƙi

  • Shugaba Donald Trump na Amurka ya yi magana game da yarjejeniyar zaman lafiya da Iran a yakin da ake yi
  • Trump ya ce Amurka ta amince da tsagaita wuta da Iran ne bayan roƙon wasu ƙasashe ba don ra’ayinta kai tsaye ba
  • Shugaban Amurka ya yi ikirarin cewa sojojin ƙasarsa sun lalata rundunar Iran gaba ɗaya, yana mai cewa har yanzu suna iya “gyara lamura” a ƙasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Washington DC, US - Shugaban Amurka, Donald Trump ya bayyana cewa ƙasarsa ta amince da tsagaita wuta da Iran ne saboda wasu ƙasashe.

Trump ya ce buƙatar wasu ƙasashe masu hulɗa da Tehran ne ya sa Amurka ta amince da tsagaita wuta.

Trump ya fadi dalilin tsagaita wuta da Iran
Jagoran addini a Iran, Mojtaba Khamenei da Shugaba Donald Trump na Amurka. Hoto: Imam Mojtaba Khamenei, Donald J Trump.
Source: Facebook

Trump ya magantu kan dalilin tsagaita wuta

Rahoton Al Jazeera ya ce Trump ya tabbatar da cewa daga cikin ƙasashen akwai Pakistan wacce ta taka rawar gani.

Kara karanta wannan

Shugaban China ya yi wa Trump gargadi kan Taiwan da suka hadu a Beijing

Trump ya ce:

“Mun amince da tsagaita wutar ne saboda wasu ƙasashe sun roƙe mu. Ni da kaina ban fi son hakan ba.”

Ya ƙara da cewa an yi hakan ne domin Pakistan, tare da haɗin gwiwar manyan shugabannin ƙasar, ciki har da firaminista da babban hafsan soji.

Trump ya sake jaddada cewa sojojin Amurka sun lalata rundunar Iran gaba ɗaya, duk da cewa har yanzu ana ci gaba da tsagaita wuta tsakanin ɓangarorin.

Ya ce bayan doguwar yarjejeniyar dakatar da yaƙi, Amurka na iya sake komawa Iran domin “maido da tsari” a wasu yankuna masu rikici.

Trump ya magantu kan dalilin tsagaita wuta a yaki da Iran
Shugaba Donald Trump na kasar Amurka. Hoto: Al Drago/Bloomberg.
Source: Getty Images

Asarar da Iran ke yi kan mashigar Hormuz

Shugaban ya ce ya amince da tsagaita wutar ne kawai saboda Amurka na gudanar da wani ƙaƙƙarfan killace hanyoyin ruwa kan Iran a yanzu.

A cewarsa, wannan killacewar ruwa na haddasa wa Iran asarar kusan dala miliyan 500 a kullum, lamarin da ke raunana tattalin arzikinta sosai.

Kara karanta wannan

Sun haura $29bn: Amurka ta fadi makudan kudaden da ta kashe a yaki da Iran

A wata hira da ya yi da Fox News ranar 14 ga Mayun 2026, Trump ya ce ya bai wa Iran zaɓi biyu kacal, cewar rahoton The Guardian.

Ya ce ko dai Iran ta cimma yarjejeniya da Amurka, ko kuma ta fuskanci cikakken barazana ta fuskar hare-haren soji daga Washington.

Trump ya bayyana cewa tun farko ya dakatar da hare-haren ne kawai saboda roƙon ƙasashen da ke da kyakkyawar alaƙa da Iran.

A wannan rana kuma, shugaban Amurkan ya wallafa a kafofin sadarwa cewa ƙasarsa za ta ci gaba da ayyukan soji kan Iran.

Yahudawa sun kai hari kan masallaci

An ji cewa wasu Yahudawa ƴan kasar Isra’ila sun kai hari a wani masallaci yayin da suka banka wuta kan motoci da ke harabar wurin ibadar.

Majiyoyi suka ce lamarin ya faru ne a kauyen Jibiya da ke kusa da Ramallah, tare da rubuta kalaman wariyar launin fata a bangon gidaje.

Maharan yahudawa sun kai hari gidajen Falasdinawa a Al-Lubban al-Sharqiya kusa da Nablus, inda suka karya kofofi da firgita mata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.