Kotu ta garkame wani uba da ke lalata da yaransa mata su 2 a Kaduna

Kotu ta garkame wani uba da ke lalata da yaransa mata su 2 a Kaduna

- Wata kotun Majistare a jahar Kaduna ta tsare wani magidanci mai suna Muhammad Isah

- Ana zarginsa da yin lalata da yaransa mata su biyu

- An tattaro cewa lamarin fyade ya yi karo na sashi na 258 na dokar jahar Kaduna ta 2017 kuma hukuncinsa na iya kasancewa daurin raid a rai yayinda a sashi na 370 na dokar kuma ya kan kasance akalla shekaru 14 a gidan yari

Wata kotun Majistare a jahar Kaduna ta tsare wani Muhammad Isah kan zargin lalata da kananan yaransa mata su biyu.

Justis Musa Lawal na kotun Majistare ya kuma dage sauraron shari’an zuwa ranar 30 ga watan Maris 2020, zuwa lokacin da zai zamana an gabatarwa da wanda ake zargin da sabbin tuhume-tuhume daga babbar kotun jahar.

Kotu ta garkame wani uba da ke lalata da yaransa mata su 2 a Kaduna
Kotu ta garkame wani uba da ke lalata da yaransa mata su 2 a Kaduna
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa lauyan mai kara, Suleiman Ibrahim Kufena ya fada ma kotu cewa an gabatar da sabbin tuhume-tuhume a gaban babbar kotun.

Sai dai wanda ake kara, wanda lauyansa Murtala Baba Ibi bai halarci zaman kotu ba ya ce shi an sanar masa da batun amma bai sani ba ko an tura umurnin kotu zuwa ga lauyansa.

An tattaro cewa lamarin fyade ya yi karo na sashi na 258 na dokar jahar Kaduna ta 2017 kuma hukuncinsa na iya kasancewa daurin raid a rai yayinda a sashi na 370 na dokar kuma ya kan kasance akalla shekaru 14 a gidan yari.

KU KARANTA KUMA: Yan bindiga sun yi garkuwa da dan wani shahararren dan kasuwa a Suleja

A wani labari na daban, mun ji cewa hukumar hana fataucin mutane ta kasa a ranar Talata, ta ce ta gurfanar wani daraktan kudi mai shekara 45 a hukumar tsare-tsaren birane da yankuna na jahar Sokoto, Ahmed Yahaya da wasu ma’aikatan hukumar biyu a gaban kotu bisa zargin lalata da wata yarinya yar shekara 12 da ke tallar ruwan leda.

Jami’in labarai na NAPTIP, Mista Vincent Adekoye, a wani jawabi, ya bayyana sauran masu laifin biyu a matsayin mai binciken kudi na gwamnatin jahar Sokoto, Mista Ibrahim Isah mai shekara 46, da mataimaki na musamman ga daraktan kudi, Mista Habibu Abdullahi mai shekara 40.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel