Oshiomhole na so ya hargitsa gwamnatina – Obaseki ya kai kukansa wajen Buhari

Oshiomhole na so ya hargitsa gwamnatina – Obaseki ya kai kukansa wajen Buhari

- Gwamnan jahar Edo, Godwin Obaseki ya zargi Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress na kasa, Adams Oshiomhole da mambobin kungiyar Edo Peoples Movement na so su hargitsa gwamnatinsa

- Obaseki dai ya kai kukansa wajen shugaban kasa Muhammadu Buhari

- Ya ce Oshiomhole da kungiyar na shirya munakisa ta yadda za su kawo rikici da rashin zaman lafiya a tsakanin mutanen Edo

Gwamnan jahar Edo, Mista Godwin Obaseki, ya koka a wajen Shugaban kasa Muhammadu Buhari, cewa Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress na kasa, Adams Oshiomhole da mambobin kungiyar Edo Peoples Movement na so su hargitsa gwamnatinsa.

Gwamna Obaseki ya ce makircin da aka ta shirya shine daukar nauyin zanga-zanga a fadin jahar a kokarin muzanta gwamnatin jahar.

Obaseki ya ce shirin kokari ne na zuga jama’a da kuma haddasa rashin aminci a jahar domin kawo koma baya a tarin ci gaban da aka samu wanda ya sa shi samun mazauni a zukatan mutanen Edo.

Oshiomhole na so ya hargitsa gwamnatina – Obaseki ya kai kukansa wajen Buhari
Oshiomhole na so ya hargitsa gwamnatina – Obaseki ya kai kukansa wajen Buhari
Asali: UGC

Gwamnan wanda ya yi magana a wata sanarwar dauke da sannun hadiminsa na musamman a kan labarai, Mista Crusoe Osagie, ya ce Oshiomhole ya yanke shawarar hada gangamin ne da tayar da kayar baya tare da kudirin haddasa rikici da kiyayya a tsakanin mutanen.

KU KARANTA KUMA: Lauyan Olisa Metuh ya yi martani kan hukuncin da aka yanke wa wanda yake karewa

Ya ce Oshiomhole da kungiyar ta EPM na kokarin sa mutane su daina biyayya da kuma tada zaune tsaye a kokarinsu na kawo rudani da rashin zaman lafiya a tsakanin mutanen Edo.

A wani labari na daban, mun ji cewa bayan hadin-kan da aka samu daga ‘Yan kungiyar Unity Forum na jam’iyyar APC a jihar Ondo, gwamna Rotimi Akeredolu, ya fito ya nuna cewa ba ya jin tsoron kowa.

‘Ya ‘yan jam’iyyar APC da ke karkashin lemar Unity Forum za su fito su tsaida ‘Dan takara guda daya tal wanda zai kara da Rotimi Akeredolu wajen samun tikitin APC.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng