Jami’an tsaro sun samo tarin makamai daga dajin Bauchi
- Jami’an tsaro da taimakon wani maharbi sun samo tarin makamai da alburusai wadanda ake zaton na yan fashi ne a dajin Lame-Burra, wani gagarumin maboyar miyagu a jahar Bauchi
- Ali Kwara wanda ya kasance tubabban dan ta’adda ne ya bayar da jawaban da ya kai su ga gano tarin makaman
- Gwamna Bala Mohammed wanda ya amshi makaman, inda shima ya mika wa yan sanda, ya ce gwamnatinsa ta yanke shawarar tattaunawa da al’umma a yaki da laifuffuka
Rahotanni sun kawo cewa jami’an tsaro da taimakon wani maharbi sun samo tarin makamai da alburusai wadanda ake zaton na yan fashi ne a dajin Lame-Burra, wani gagarumin maboyar miyagu a jahar Bauchi.
A cewar maharbin, Ali Kwara wanda ya kasance tubabban dan ta’adda ne ya bayar da jawaban da ya kai su ga gano tarin makaman, Channels TV ta ruwaito.
Tarin makaman yan ta’addan, wanda aka baje a gidan gwamnatin auchi sun hada da alburusai sama da guda 1,000, makamai iri daban-daban guda 43 da kuma harsasai 30, koda dai su kansu yan ta’addan suna da yawa.

Asali: UGC
Gwamna Bala Mohammed wanda ya amshi makaman, inda shima ya mika wa yan sanda, ya ce gwamnatinsa ta yanke shawarar tattaunawa da al’umma a yaki da laifuffuka.
Ya bayyana cewa an gano makaman ne sakamakon kwarewar hukumar tsaro ta SSS da sauran hukumomin tsaro.

Asali: UGC
“Tare da hadin gwiwar yan sanda, mun kwato wannan dagan yan bindiga da suka kasance da yawa sannan sun tsere daga Bauchi.
KU KARANTA KUMA: Kotu ta garkame wani uba da ke lalata da yaransa mata su 2 a Kaduna

Asali: UGC
“Akwai wasu yan leken asiri a ciki da wajen garin Bauchi da kewayenta wadanda suke taimaka mana wajen yin haka kuma wannan hadin gwiwa ne tsakanin gwamnati, Ali Kwara da hukumomin tsaron saboda mu samu damar samun zantawa sosai da al’umma tare da wani kudirin sanin dukkanin wadannan yan bindigan,” in ji shi.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng