'Ka Yi Hattara,' Malami Ya Hango Wasu Gwamnonin Arewa Za Su Yaudari Tinubu a 2027

'Ka Yi Hattara,' Malami Ya Hango Wasu Gwamnonin Arewa Za Su Yaudari Tinubu a 2027

  • Primate Elijah Ayodele ya gargadi Shugaba Bola Tinubu da kada ya dogara kacokan kan gwamnonin Arewa wajen neman tazarce a zaɓen 2027
  • Babban malamin addinin Kiristan ya yi zargin cewa wasu daga cikin gwamnonin na da manufofin kansu da za su iya kawo cikas ga burin Tinubu
  • Ya kuma yi hasashen cewa zaɓukan fitar da gwani da jam’iyyu za su gudanar kwanan nan zai zamo silar faɗuwar wasu manyan ‘yan siyasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Legas - Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual, Primate Elijah Ayodele, ya gargadi Shugaba Bola Tinubu da kada ya dogara kacokan kan gwamnonin Arewa wajen shirinsa na neman tazarce a 2027.

Primate Ayodele ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Osho Oluwatosin, ya sanyawa hannu.

Kara karanta wannan

Bayan tadiye yaransa a tantancewar APC, Fubara ya magantu kan alakarsa da jam'iyya

Primate Elijah Ayodele ya gargadi Shugaba Bola Tinubu kan gwamnonin Arewa a 2027.
Primate Babatunde Elijah Ayodele da Shugaba Bola Ahmed Tinubu. Hoto: Primate Babatunde Elijah Ayodele, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Source: Facebook

An gargadi Tinubu kan gwamnonin Arewa

Babban malamin addinin Kiristan ya yi zargin cewa ba dukkan gwamnonin Arewa ne ke goyon bayan burin Tinubu na sake tsayawa takara ba, in ji rahoton Tribune.

A cewar Ayodele, wasu daga cikin gwamnonin suna da manufofin siyasa na kansu da za su iya yin illa ga shirin shugaban ƙasar.

“Ya kamata Shugaba Tinubu ya yi hattara kada wasu gwamnonin Arewa su juya masa baya a dab zabe. Ba dukansu ne suke tare da shi wajen neman tazarce ba,” in ji Ayodele.

Ya ƙara da cewa idan shugaban bai kula da abubuwan da ke faruwa a cikin sansanin siyasarsa ba, hakan na iya janyo masa matsaloli.

'Wasu za su ci amanar Tinubu' - Ayodele

Malamin ya kuma yi gargadin cewa wasu daga cikin mutanen da ke nuna biyayya ga shugaban na iya ba shi mamaki a gaba.

Primate Ayodele ya bayyana cewa:

Kara karanta wannan

Atiku ya 'bankado' shirin gwamnoni game da tazarcen Tinubu a zaben 2027

“Da yawa daga cikinsu suna da ajandarsu. Idan shugaban bai yi hankali ba, cin amanarsu zai iya lalata burinsa na siyasa."

Ya buƙaci Tinubu da ya kasance cikin shiri tare da sa ido sosai kan masu kusa da shi.

Primate Elijah Ayodele ya yi hasashen cewa za a samu rigingimu a jam'iyyu bayan zaben fitar da gwani
Primate Elijah Ayodele ya na magana a ofishinsa da ke cikin cocin INRI Evangelical. Hoto: Primate Babatunde Elijah Ayodele
Source: Facebook

Malami ya hango rikici a jam'iyyu

Primate Ayodele ya kuma yi hasashen cewa zaɓukan fitar da gwani na jam’iyyun siyasa za su haifar da nakasu ga wasu fitattun ‘yan siyasa a ƙasar, kamar yadda Punch ta ruwaito.

A cewarsa, mutane masu ƙarfi a jam’iyyu daban-daban har da APC za su rasa kujerun da suke kai, yayin da sababbin shiga kuma ba za su samu tikitin da suke nema ba.

“Mutane da dama za su yi kuka da jam'iyyyunsu bayan zaɓen fitar da gwani. Wasu manyan mutane za su faɗi, har ma a cikin APC."

- Primate Elijah Ayodele.

Kalaman malamin na zuwa ne yayin da ake ci gaba da tattaunawa kan yadda jam’iyyun Najeriya ke tunkarar babban zaɓe na shekarar 2027.

'Za a hana Tinubu tazarce' - Ayodele

Kara karanta wannan

Atiku ya dura kan Tinubu da ƴan bindiga suka kashe tsohon ɗan majalisar Jigawa

A wani labari, mun ruwaito cewa, Primate Elijah Ayodele ya yi hasashen cewa manyan ƙasashe kamar Amurka da Birtaniya za su goyi bayan jam'iyyun hamayya a 2027.

Malamin addinin ya bayyana cewa kodayake Shugaba Bola Tinubu yana da dukkan dabarun lashe zaɓe, cikas ɗinsa mafi girma zai fito ne daga ƙasashen waje.

Primate Ayodele, shugaban cocin INRI Evengelical Spiritual ya gargaɗi jam'iyyun hamayya cewa muddin suka raba kansu, ba za su taɓa iya kayar da Tinubu ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com