Yanzu Yanzu: Dan Italiyan da ke dauke da cutar Coronavirus ya ziyarci Ogun

Yanzu Yanzu: Dan Italiyan da ke dauke da cutar Coronavirus ya ziyarci Ogun

Sabbin bayanai sun bayyana cewa dan italiyan da ke dauke da cutar Coronavirus ya ziyarci jahar Ogun kafin a kai shi Lagas inda aka tabbatar da cewar yana dauke da cutar.

An tattaro cewa Dan kasar Italiyan, wanda ya shigo Najeriya ta jirgin Turkiyya, ya nuna alamun cutar a jahar Ogun kafin aka yi gaggawan kais hi Lagas domin yin bincike a tsanaki a cibiyar kula da cututtuka ta Najeriya a Yaba.

Da yake jawabi ga manema labarai a fadar gwamnati Marina, Gwamna Babajide Sanwo-Olu tare da kwamishinan lafiya na jahar, Farfesa Akin Abayomi ya bayyana cewa mutumin bai nuna kowani alama na cutar Coronavirus ba da farko.

Su biyun sun bukaci mutane da su cire tsoro kan barkewar annobar inda suka bayar da tabbacin cewa an kebe mara lafiyan. Sai dai sun ki magana kan yawan mutanen da aka gano ya yi hulda dasu ko kuma wadanda ake ganin sun hadu da mutumin a lokacin zamansa a Ogun ko Lagas.

Har ila yau mun jicewa dan kasar Italiyan ya ziyarci Ewekoro a karamar hukumar Ewekoro da ke jahar Ogun a wannan makon.

Sai dai kwamishinan lafiya, Tomi Coker a safiyar ranar Juma’a, 28 ga watan Fabrairu ta bayyana cewa kada mazauna da baki a jahar su daga hankalinsu.

Coker ta bayyana cewa mutumin na kasar Italiya ya ziyarci wani babban kamfani wanda aka sakaya sunansa a garin Ekwekoro, inda ta kara da cewar tuni aka kebe kamfanin da ya ziyarta daidai da tsarin kiyayewar lafiya.

Yanzu Yanzu: Dan Italiyan da ke dauke da cutar Coronavirus ya ziyarci Ogun
Yanzu Yanzu: Dan Italiyan da ke dauke da cutar Coronavirus ya ziyarci Ogun
Asali: Twitter

Kwamishinan, wacce ta hana kanta bacci domin kula da lafiyar jama’a na gaggawa, yayinda ta ke jawabi ga manema labarai, ta ce tuni jahar ta tanadi likitocin da ke kan kula da lamarin da taimakon gwamnatin jahar Lagas da na tarayya.

Ta ce ana kan kokarin ganin an isa ga mutanen da ya yi hulda dasu.

Ta shawarci jama’a da su yawaita wanke hannuwansu, da rufe bakuna da hancinsu a yayinda suke atishawa da tari sannan su isa ga cibiyar lafiya mafi kusa da zaran sun ga wani alama na sanyi, mura ko wuya wajen jan numfashi.

KU KARANTA KUMA: Jerin manyan kasashen Turai da Coronavirus ta ratsa a Duniya

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto a baya cewa Gwamnatin jihar Legas ta ce jamianta sun bazama neman dukkan wadanda dan kasar Italiyan da ya kawo cutar Najeriya ya hadu da su tun ranar da ya shigo.

Kwamishanan kiwon lafiyar jihar, Farfesa Akin Abayomi, ya bayyana hakan inda ya ce an kebance mutumin kuma ana kula da shi.

Yace: “Ku sani cewa duk wanda ya kamu da cutar zai iya fuskantar dan zazzabi kuma ya warke, amma zai iya tsanani a wasu, musamman tsofaffi.Mun kaddamar da ayyukan gaggawa domin kange cutar da hana yaduwa.

“Muna tabbatarwa dukkan mutan jihar Legas da Najeriya cewa tun lokacin da cutar ta bulla a kasar Sin muke shiryawa. Zamuyi amfani da dukkan dukiyar da muke da shi tare da gwamnatin tarayya wajen dakile lamarin."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel