Wasu 'Yan Kasashen Waje da Ake Zargi da Hannu a Ta'addanci Sun Shiga Hannun NSA a Najeriya

Wasu 'Yan Kasashen Waje da Ake Zargi da Hannu a Ta'addanci Sun Shiga Hannun NSA a Najeriya

  • Gwamnatin tarayya ta tabbatar da kama yan kasashen waje bisa zargin hakar ma'adanai ba bisa ka'ida ba da taimaka wa ta'addanci
  • Ministan ma'adanai, Dele Alake ya bayyana cewa an mika wadanda aka cafke ga ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro
  • Duk da bai bayyana adadin da aka mika wa NSA ba, Alake ya ce an kama sama da mutum 327 da ake zargi da haƙar ma’adanai ba bisa ka'ida ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Ministan Harkokin Ma’adanai, Dele Alake, ya bayyana cewa an cafke wasu baƙi daga ƙasashen waje suna gudanar da haƙar ma’adanai ba bisa ka’ida ba, kuma ana zargin suna da alaƙa da tallafa wa ayyukan ta’addanci.

Ministan ya tabbatar da kama mutanen tare da mika su ga Ofishin Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara Kan Harkokin Tsaro (NSA), Malam Nuhu Ribadu domin ci gaba da bincike.

Kara karanta wannan

Sun haura $29bn: Amurka ta fadi makudan kudaden da ta kashe a yaki da Iran

Dele Alake.
Ministan harkokin ma'adanai, Dele Alake a wurin taro kan batun bunkasa fannin ma'adanan Najeriya Hoto: Dele Alake
Source: Twitter

Alake ya bayyana hakan ne ranar Juma’a, 15 ga watan Mayu, 2025 yayin da yake amsa tambayoyi daga gidan talabijin na Channels tv a wani taro da aka gudanar a Abuja.

An gudanar da taron ne kan zarge-zargen da wasu ‘yan majalisar dokokin Amurka suka yi, inda suka danganta haƙar ma’adanai ba bisa ka’ida da wasu ‘yan ƙasar China ke yi da tallafa wa ayyukan ta’addanci a Najeriya.

An kama 'yan kasashen waje a Najeriya

Ko da yake bai bayyana adadin yan ƙasashen da aka miƙa wa ofishin NSA ba, ministan ya ce an kama sama da mutum 327 da ake zargi da haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba.

Dele Alake ya ce kusan mutum 142 daga cikinsu sun fara fuskantar shari’a, sannan an soke lasisin haƙar ma’adanai na kimanin mutane 3,000.

Ya danganta nasarorin da aka samu a ɓangaren ma’adanai, ciki har da ƙarin kuɗaɗen shiga daga Naira biliyan shida a shekarar 2023 zuwa sama da Naira biliyan 70 a 2025.

Kara karanta wannan

Hankula sun tashi da 'yan ta'adda suka tare matafiya a Zamfara, an tafka barna

Ministan ya ce nasarorin da aka samu a ɓangaren ma’adanai da sauran fannoni na tattalin arziki sun nuna cewa gyaran da gwamnatin Tinubu ke yi zai taimaka wajen kawo ƙarshen cin hanci da rashawa da raunin cibiyoyi a Najeriya.

Nuhu Ribadu.
Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaron Najeriya, Malam Nuhu Ribadu Hoto: Nuhu Ribadu
Source: Facebook

Alake ya ja hankalin masu hakar ma'adanai

Yayin jawabi ga masu ruwa da tsaki da masu harkokin ma’adanai, Alake ya buƙaci su kasance masu kishin ƙasa domin bunƙasa fannin zuwa mataki mafi girma, cewar Punch.

A ƙarshen shekarar da ta gabata, Shugaba Bola Tinubu ya nuna damuwa kan yadda ake ci gaba da wawure albarkatun ma’adanai, yana mai cewa hakan yana barazana ga zaman lafiyar yankin Afirka ta Yamma.

Kotu ta yanke wa dan ta'adda hukunci

A wani labarin, kun ji cewa wata kotu da ke zamanta a birnin Abuja ta fara yanke hukunci kan wasu daga cikin kwamandojin kungiyar Ansaru da aka kama kwanakin baya.

Kotun ta yanke wa kwamandan, Mahmud Usman, hukuncin daurin shekaru 15 a gidan gyaran hali bayan samun shi da laifuffuka da suka shafi ta'addanci.

Hukumar DSS ce ta gurfanar Usman, wanda ya amsa laifin hakar ma'adinai ba bisa ka'ida ba da aka ce ya taimaka masa wajen samun.makamai don ta’addanci da satar mutane.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262