Ya Kamata Ku Sani: Abu 4 da Za Su Fi Ɗaukar Hankali a Ziyarar Trump zuwa China

Ya Kamata Ku Sani: Abu 4 da Za Su Fi Ɗaukar Hankali a Ziyarar Trump zuwa China

China - An tsaurara matakan tsaro a tsakiyar birnin Beijing, musamman ma dandalin Tiananmen yayin da shugaban Amurka, Donald Trump ya kai ziyara kasar China.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Rahotanni sun nuna cewa Donald Trump da Xi Jinping sun fara shirya ziyarar ne cikin sirri kafin daga baya gwamnatin China ta fito da batun shirin karbar shugaban Amurkan a fili.

Trump ya ziyarci China inda ake fatan za a gyara alakar Amurka da birnin Sin.
Shugaban Amurka Donald Trump da Shugaban China, Xi Jinping a Beijing. Hoto: Kenny HOLSTON / POOL / AFP via Getty Images
Source: Getty Images

Trump da Xi na neman kyautata alaka

BBC Hausa ta ruwaito cewa ziyarar za ta kunshi tattaunawa mai muhimmanci, kwarya kwaryar liyafar cin abinci, har ma da ziyartar wasu wuraren tarihi da wuraren bautar addini na kasar China.

Donald Trump da Xi Jinping, na fatan ziyarar za ta taimaka wajen rage zaman dar-dar da aka dade ana fama da shi tsakanin kasashensu biyu.

Rahoton ya nuna cewa wannan ce ganawa ta farko tsakanin shugabannin cikin shekaru masu yawa, yayin da ake kallon su a matsayin manyan abokan hamayya a siyasa da tattalin arziki.

Kara karanta wannan

Sulhu ko kato bayan kato: Jam'iyyar APC ta kaddamar da fara zaben fitar da gwani

A baya, Trump bai nuna wata babbar sha’awa wajen kyautata alakar Amurka da China ba, sai dai sababbin matsalolin da ke addabar wasu sassan duniya sun sauya yanayin siyasar.

Abubuwan da za su ja hankali a ziyarar

Ga wasu abubuwa 4 da za su fi daukar hankali a ziyarar Trump zuwa China:

1. Matsayar China kan yakin Iran

Daya daga cikin manyan batutuwan da za su mamaye tattaunawar shi ne yakin Iran da ke ci gaba da daukar hankali a Gabas ta Tsakiya.

China na kokarin taka rawar sulhu domin kawo karshen rikicin, inda ta hada kai da kasar Pakistan a gabatar da shawarwari domin tsagaita wuta da sake bude mashigar Hormuz.

Rahotanni sun nuna cewa jami’an Iran sun ci gaba da tattaunawa da China domin neman mafita, kamar yadda rahoton NBC ya nuna.

Masana sun bayyana cewa China na fuskantar matsin tattalin arziki saboda dogaro da man fetur daga Iran.

A nata bangaren, Amurka na son China ta taimaka wajen matsa wa Iran domin dawo da ita teburin tattaunawa.

2. Makomar Taiwan

Kara karanta wannan

Kotu ta yanke wa malamin addinin Musulunci daurin rai da rai a Birtaniya

Trump ya kai ziyara kasar China.
Shugaba Donald Trump da Shugaba Xi Jinping sun halarci taron hadin gwiwar Amurka da China a Great Hall of the People, a Beijing. Hoto: Alex Wong/Getty Images
Source: Getty Images

Batun Taiwan ma na daga cikin manyan abubuwan da ake sa ran Donald Trump da Xi Jinping za su tattauna.

A baya gwamnatin Trump ta amince da tallafin makamai na biliyoyin daloli ga Taiwan, lamarin da ya fusata China.

Sai dai daga baya Trump ya nuna cewa Amurka ba za ta tsoma baki kai tsaye wajen kare Taiwan ba.

China na kallon Taiwan a matsayin wani bangare nata, yayin da Amurka ke ci gaba da nuna goyon baya ga yankin.

Ko a wannan taron, Aljazeera ta rahoto cewa China ta gargadi Amurka da ta tsame hannunta, ta kuma kawar da kai daga abin da ya shafi Taiwan.

3. Rikicin kasuwanci

Kasuwanci tsakanin Amurka da China ya kasance cikin rikici tsawon shekararu kusan biyu. Lamarin ya yi muni ne musamman daga 2025.

Trump ya kara haraji kan kayayyakin China sau da dama, yayin da China ta mayar da martani ta rage sayen wasu kayayyakin Amurka.

Kara karanta wannan

Hajjin 2026: Kasar Saudiyya ta yi gyare gyare, ta tura tallafi ga kasashen Musulmi 27

Lamarin ya shafi tattalin arzikin duniya tare da jefa manoma da kamfanoni cikin matsin hali bayan dawowar Donald Trump kan mulki.

Masana na ganin ziyarar za ta bai wa kasashen damar sake bude tattaunawa domin rage rikicin kasuwanci.

Ana sa ran Trump zai matsa wa China ta kara sayen kayan gona daga Amurka, yayin da China ke son rage mata harajin da aka kakaba mata.

Ana 'yan awanni kafin ziyarar, China ta sanar da dawo da kasuwancin nama da Amurka, don nuna hobbasarta ga nasarorin da ziyarar za ta haifar, in ji rahoton The New York Times.

4. Gasar fasahar AI

Ana sa ran China da Amurka za su tattauna kan fasahar AI da suke samun sabani a kai.
Tutar kasar China a jikin waya kusa da fasahar AI. Hoto: Budrul Chukrut/SOPA Images/LightRocket via Getty Images
Source: Getty Images

Fasahar AI na daya daga cikin manyan wuraren da Amurka da China ke fafatawa. China na zuba makudan kudade wajen bunkasa fasahar AI da kirkirar mutum-mutumin zamani masu aiki irin na dan Adam.

Sai dai Amurka na zargin China da amfani da fasahohinta wajen bunkasa shirye-shiryenta. Saboda haka gwamnatin Amurka ta takaita fitar da wasu fasahohi zuwa China.

Masana sun ce ganawar Trump da Xi na iya taimakawa wajen rage takaddama kan amfani da AI da sauran manyan fasahohi.

Kara karanta wannan

Yadda aka tatsi bayanai daga wadanda ake zargi da shirya juyin mulkin Tinubu

China gargadi Amurka kan alakar Taiwan

Tun da fari, mun ruwaito cewa, Shugaban China, Xi Jinping ya gargaɗi takwaransa na Amurka, Donald Trump, kan batun Taiwan a taron ƙasashen biyu.

A bayanin da ya yi, Xi Jinping ya gargaɗi Donald Trump cewa idan ya yi wani kuskure game da Taiwan zai iya jefa ƙasashen biyu cikin babban rikici.

Ya fadi haka ne yayin da shugabannin biyu suka gana a birnin Beijing ranar Alhamis, 14 ga watan Mayun 2026 a taron manyan ƙasashen biyu masu ƙarfi a duniya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com