Yanzun-nan: Kotu ta kaddamar da tsige tsohon mataimakin gwamnan Kogi Achuba a matsayin ba bisa doka ba

Yanzun-nan: Kotu ta kaddamar da tsige tsohon mataimakin gwamnan Kogi Achuba a matsayin ba bisa doka ba

- Babbar kotun jahar Kogi a Lokoja ta kaddamar da tsige Simon Achuba, tsohon mataimakin gwamnan Kogi da majalisar dokokin jahar ta yi a matsayin sokakke

- Alkalin kotun ya ce tsige Achuba daga kujerarsa da majalisar dokokin ta yi ya saba ma kundin tsarin mulki

- Ya kuma ce ba a bi tsarin da ya kamata ba wajen zabar Edward Onoja a matsayin mataimakin Gwamna

Wata babbar kotun jaha a Lokoja ta kaddamar da tsige Simon Achuba, tsohon mataimakin gwamnan Kogi da majalisar dokokin jahar ta yi a matsayin sokakke.

Justis John Olorunfemi yayinda ya ke zartar da hukunci a ranar Laraba, ya ce tsige Achuba daga kujerarsa da majalisar dokokin ta yi ya saba ma kundin tsarin mulki kuma hakazalika ba a bi tsarin da ya kamata ba wajen zabar Edward Onoja a matsayin mataimakin Gwamna.

Justis Olorunfemi ya bayyana matakin majalisar dokokin jahar Kogi a matsayin wani yuyin kundin tsarin mulki, wanda ya kasance take damokradiyya, inda ya kara da cewa hakan ya saba na sashi na 188 karamin sashi na 8, wanda ya hana Majalisar dokoki ci gaba da matakin bayan ta gano cewa tsohon mataimakin gwamnan bai yi kowani laifi ba ga majalisar.

Yanzun-nan: Kotu ta kaddamar da tsige tsohon mataimakin gwamnan Kogi Achuba a matsayin ba bisa doka ba
Yanzun-nan: Kotu ta kaddamar da tsige tsohon mataimakin gwamnan Kogi Achuba a matsayin ba bisa doka ba
Asali: UGC

KU KARANTA KUMA: Mahaifiyar Leah Sharibu ta yi wa Landan tsinke don ganawa da Firaministan Birtaniya

Da farko dai Achuba ya kalubalanci tsige shi da majalisar dokokin jahar Kogi ta yi sannan ya nemi kotu da ya kaddamar da tsigewar nasa a matsayin wanda ba ya bisa ka’ida sannan ta dawo dashi a matsayin mataimakin gwamnan jahar.

Majalisar dokokin jahar Kogi ce dai tsige Achuba ne a watan Oktoba 2019.

A wani labari na daban, mun ji cewa Shugabannin jam’iyyar PDP za su yi wani zama na musamman a sakamakon taron gaggawar da aka kira wanda za a yi Yau Alhamis a Garin Abuja.

Kamar yadda sanarwar ta nuna, majalisar NEC za ta yi wani zaman gaggawa ne a babban Hedikwatar jam’iyyar da ke Wadata Plaza a Abuja.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel