Mugwayen mutanen da ke Najeriya sun ki mutuwa - Sanata Abaribe

Mugwayen mutanen da ke Najeriya sun ki mutuwa - Sanata Abaribe

- Sanata Enyinnya Abaribe, ya ce mugwayen mutane a Najeriya sun ki mutuwa yayinda kasar ke ci gaba da rasa salihan al’ummanta

- Ya fadi hakan ne a ranar Laraba, 26 ga watan Fabrairu, a wani taro da aka shirya don karrama marigayi Sanata Ignatius Longjan

- Abaribe ya bayyana Longjan a matsayin mutumin kirki sosai yayin da ya yi wa matar dan majalisar da yara da mutanen da yake wakilta ta’aziyya

Sanata Enyinnya Abaribe, ya ce mugwayen mutane a Najeriya sun ki mutuwa yayinda kasar ke ci gaba da rasa salihan al’ummanta.

Shugaban marasa rinjaye a majalisa ya fadi hakan ne a ranar Laraba, 26 ga watan Fabrairu, a wani taro da aka shirya don karrama marigayi Sanata Ignatius Longjan.

Mugwayen mutanen da ke Najeriya sun ki mutuwa - Sanata Abaribe
Mugwayen mutanen da ke Najeriya sun ki mutuwa - Sanata Abaribe
Asali: UGC

“Duk da haka mun sake rasa wani mutumin kirki. Tambayar da muke tambaya a koda yaushe shine manene dailin da yasa muke rasa mutanen kirki? Mugwayen mutane a kasar nan basa mutuwa, mutanen kirki ne ke tafiya,” in ji Abaribe.

Abaribe ya bayyana Longjan a matsayin mutumin kirki sosai yayin da ya yi wa matar dan majalisar da yara da mutanen da yake wakilta ta’aziyya.

Dan majalisar ya kuma yi ta’aziyya ga al’umman yankin da Longjan ya fito da yan Najeriya baki daya.

Sanata Longjan wanda ke wakiltan Plateau ta kudu ya rasu a ranar 10 ga watan Fabrairu a Abuja.

KU KARANTA KUMA: Mahaifiyar Leah Sharibu ta yi wa Landan tsinke don ganawa da Firaministan Birtaniya

A wani labari na daban, mun ji cewa Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya rattaba hannu a kan dokar zartar da hukuncin kisa ga duk wanda aka samu da laifin garkuwa da mutane a jihar.

"Majalisar dokokin jihar Nasarawa ta gudanar da mahawara tare da yin duba na tsanaki kafin su amince da dokar.

"Dokar ta ayyana laifuka masu nasaba da garkuwa da mutane da kuma kunshin hukunce-hukuncensu. Daga cikin hukuncin akwai dauri a gidan yari da hukuncin kisa," a cewar gwamnan.

Gwamna Sule ya bayyana cewa gwamnati za ta mallaki duk wata kaddara ta wanda aka samu da laifin garkuwa da mutane. Kazalika, ya bayyana cewa masu bayar da hayan wurin zama ga masu garkuwa da mutanen, za su iya fuskantar hukuncin daurin shekaru 20 a gidan yari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel