2027: Tsohon Shugaban INEC Ya Samu Tikiti, Zai Tsaya Takarar Gwamnan Yobe a ADC

2027: Tsohon Shugaban INEC Ya Samu Tikiti, Zai Tsaya Takarar Gwamnan Yobe a ADC

  • Jam’iyyar ADC a jihar Yobe ta ayyana Kassim Gana Geidam a matsayin ɗan takarar gwamna na bai ɗaya domin zaɓen shekarar 2027
  • Jam’iyyar ta ce an cimma matsayar ne bayan tattaunawa tsakanin shugabanni da masu neman takara domin tabbatar da haɗin kai
  • Haka kuma, takarar tsohon shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan ta samu cikas bayan manyan APC sun marawa Baba Wali baya a Yobe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Yobe - Jam’iyyar ADC reshen jihar Yobe ta bayyana Kassim Gana Geidam a matsayin ɗan takarar gwamna na bai ɗaya domin babban zaɓen shekarar 2027.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren jam’iyyar a jihar, Mamu Alhaji Muhammad, ya fitar ranar Juma’a a Damaturu.

Jam'iyyar ADC ta tsaya rda d'an takarar gwamnan Yobe.
Jam'iyyar ADC ta tsayar da Barista Kassim Gana Geidam a matsayin dan takarar gwamnan Yobe. Hoto: @Inside_Yobe, @BolajiADC
Source: Twitter

ADC ta tsayar da dan takara a Yobe

Sanarwar ta bayyana cewa zabar Geidam ta biyo bayan doguwar tattaunawa tsakanin shugabannin jam’iyyar da masu neman takara gabanin zaɓen 2027, in ji rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Takarar 2027: 'Yan APC sun barke da zanga zanga, an yi fashe fashe a Oyo

ADC ta yabawa waɗanda suka janye daga neman tikitin takara domin goyon bayan tsarin sasanci da aka cimma. Jam’iyyar ta bayyana matakin a matsayin nuna biyayya, sadaukarwa da kishin haɗin kan jam’iyyar da ci gaban jihar.

Jam’iyyar ta bayyana Kassim Geidam a matsayin gogaggen jami’in gwamnati, lauya kuma ƙwararren masani da ya daɗe yana hidima a fannoni daban-daban.

Ta ce ya taɓa zama kwamishinan zaɓe mai zaman kansa na INEC, Antoni Janar kuma kwamishinan shari’a.

"Haka kuma ya kasance shugaban farko na kamfanin Yobe Line da kuma shugaban farko na ƙaramar hukumar Yusufari," in ji sanarwar ADC.

ADC ta jaddada cancantar Kassim Geidam

ADC ta kuma tuna cewa Geidam na cikin kwamitin tsara kundin mulki a taron ƙasa na shekarar 1994 wanda ya taimaka wajen samar da kundin tsarin mulkin 1999.

A bangaren harkokin banki kuwa, jam’iyyar ta ce ya riƙe manyan mukamai a Habib Nigeria Bank Limited, ciki har da shugaban sashen shari’a da daraktan yanki.

Jam’iyyar ta bayyana Geidam a matsayin mutum mai haɗa kan al’umma ba tare da la’akari da bambancin ƙabila ko yanki ba, in ji rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Tsohon mataimakin gwamna ya samu tikitin takara, zai kara da Gwamnan Sokoto

Ta ce an san shi da tawali’u da sauƙin kai tare da jajircewa wajen gudanar da mulki mai adalci da haɗa kowa da kowa. Saboda haka jam’iyyar ta bukaci mambobinta da mazauna jihar su mara masa baya a zaɓen gwamnan shekarar 2027.

Tuni ADC da APC suka ayyana 'yan takarar su na gwamna a zaben jihar Yobe
Taswirar jihar Yobe da ke a Arewa maso Gabashin Najeriya. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Takarar Ahmad Lawan ta gamu da cikas

A wani labaran makamancin wannan, jaridar Premium Times ta rahoto cewa cewa burin tsohon shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, na tsayawa takarar gwamna a APC ya samu cikas.

Hakan ya biyo bayan amincewar manyan masu ruwa da tsaki a APC kan Baba Wali a matsayin wanda za su marawa baya a matsayin dan takara a zaben jihar Yobe na 2027.

Rahotanni sun nuna cewa gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, da ministan harkokin ‘yan sanda, Ibrahim Gaidam, sun haɗa kai wajen goyon bayan Baba Wali.

Tsohon IGP ya fasa takarar gwamnan Yobe

A wani labari, mun ruwaito cewa, mutanen da ke neman samun takarar gwamnan jihar Yobe karkashin inuwar jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya sun rage yawa.

Tsohon shugaban 'yan sandan Najeriya, Usman Alkali Baba, ya sanar da janyewarsa daga neman takarar gwamnan Yobe a inuwar APC.

Usman Alkali Baba ya bayyana cewa matakin janyewar ya kasance mai wahala amma wanda ya zama dole domin samar da hadin kai da ci gaban jihar Yobe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com