Yan bindiga sun yi garkuwa da dan wani shahararren dan kasuwa a Suleja

Yan bindiga sun yi garkuwa da dan wani shahararren dan kasuwa a Suleja

- Yan bindiga da ake zaton masu garkuwa da mutane ne sun sace yaron wani dan kasuwa a Suleja a Chaza, wani gari da ke wajen garin Suleja a jahar Niger

- Yaron mai suna, Shafiu Sani, na kula da wasu abokan kasuwanci ne lokacin da yan bindigan wadanda suka bude wuta suka isa wajen, sannan suka shiga shagonsa inda suka tisa keyarsa

- An tattaro cewa wasu yan watanni da suka gabata ne aka yi garkuwa da mahaifin yaron wanda aka bayyana a matsayin Alhaji Sani

Wasu yan bindiga da ake zaton masu garkuwa da mutane ne sun sace yaron wani dan kasuwa a Suleja a Chaza, wani gari da ke wajen garin Suleja a jahar Niger.

An tattaro cewa yaron, Shafiu Sani, na kula da wasu abokan kasuwanci ne lokacin da yan bindigan wadanda suka bude wuta suka isa wajen, sannan suka shiga shagonsa inda suka tisa keyarsa.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa wasu yan watanni da suka gabata ne aka yi garkuwa da mahaifin yaron wanda aka bayyana a matsayin Alhaji Sani.

Yan bindiga sun yi garkuwa da dan wani shahararren dan kasuwa a Suleja
Yan bindiga sun yi garkuwa da dan wani shahararren dan kasuwa a Suleja
Asali: Twitter

Wani idon shaida wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce ga dukkan alamu yan bindigar na ta bibiyar dan kasuwan wanda ya iso yankin daga garin Suleja inda yake da zama, yan mintuna bayan karfe 8:00 na dare, lokacin da abun ya faru a ranar Juma’a da ya gabata.

Shugaban kungiyar yan banga a kauyen, Dantani Jarumai, ya yi bayanin yadda suka samu bayanin lamarin.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: An dakatar da hadimin Obaseki daga APC

“Mun idar da sallarmu na dare kenan, sannan mun yi zaman cin abincin dare tare da wasu abokan aikina, lokacin da muka jiyo karar harbin bindiga daga yankin kauyen.

“Sai na fada wa yara na cewa kamar akwai tashin hankali a garin amma na muka isa wajen bamu ga kowa ba sannan muka gano cewa sun tafi,” in ji shi.

A wani labarin kuma, mun ji cewa babban sifeton rundunar 'yan sanda na kasa (IGP), Mohammed Adamu, ya bayar da umarnin rufe wasu ofisoshin tawagar 'yan sanda na musamman da ke yaki da fashi da makami (SARS) da ke fadin Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel