Matashi ya boye a cikin banki har dare yayi kowa ya tashi a aiki domin ya saci N340,000

Matashi ya boye a cikin banki har dare yayi kowa ya tashi a aiki domin ya saci N340,000

- Wani matashi dan shekara 16 ya gurfana a gaban kotun majistare na Igbosere da ke jahar Lagas kan zargin boyewa a cikin bayin wani banki tsakar dare sannan ya saci kudi naira 340,000

- Jami’an tsaron bankin ne suka kama mai laifin da misalin karfe 2:30 na tsakar dare bayan ya yi yunkurin tserewa daga bankin

- Matashin ya samu shiga bankin ne a daidai lokacin da ake hada-hadar tashi daga aiki kafin karfe 4:00 na rana sannan ya boye a bandaki har kafa ya dauke

An gurfanar da wani matashi dan shekara 16 a gaban kotun majistare na Igbosere da ke jahar Lagas kan zargin boyewa a cikin bayin wani banki tsakar dare sannan ya saci kudi naira 340,000.

Yan sandan Ajah ne suka gurfanar da matashin da aka saya sunansa wanda ya fito daga unguwar Abimbola, Even Estate, Ajah, Lagas kan zargin yin sata.

Dan sanda mai kara, Sufeto Peace Chukwudi ya fada ma kotu a karar mai lamba C/09/2020 cewa wanda ake karan ya aikata laifin ne a ranar 19 ga watan Fabrairu.

Matashi ya boye a cikin banki har dare yayi kowa ya tashi a aiki domin ya saci N340,000
Matashi ya boye a cikin banki har dare yayi kowa ya tashi a aiki domin ya saci N340,000
Asali: Twitter

Ya yi zargin cewa an jami’an tsaron bankin ne suka kama mai laifin.

Chukwudi ya ce da ake masa tambayoyi, yaron ya tona cewa ya samu shiga bankin ne kafin karfe 4:00 na rana, lokacin da ake hada-hadar rufe bankin.

Sai ya shiga cikin bandaki ya boye har sai da kowa ya tafi.

Kotun ta ji cewa yaron ya bude wajen ajiyar ma’aikata da misalin karfe 2:30 na tsakar dare inda ya samu N340,000 a ciki sannan ya boye a cikin rigarsa.

Ya yi kokarin guduwa daga bankin amma sai masu gadin bankin suka gano shi sannan suka kama shi.

A cewar Chukwudi laifin na da hukunci a karkashin sashi 28 na dokar laifin jahar Lagas, 2015.

KU KARANTA KUMA: Soyayya ce ta jani, shi kuma saurayina ya koya mini garkuwa da mutane - Cewar Hassana

Wanda ake karan bai amsa laifinsa ba.

Mai shari’a Doja-Ojo ta tsare shi a gidan gyara halayya na Oregun Juvenile, Ikeja.

Ta dage sauraron karar zuwa 15 ga watan Afrilu don hujja da yanke hukunci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel