Mahaifiyar Leah Sharibu ta yi wa Landan tsinke don ganawa da Firaministan Birtaniya

Mahaifiyar Leah Sharibu ta yi wa Landan tsinke don ganawa da Firaministan Birtaniya

- Mahaifiyar Leah Sharibu, yarinyar makarantar Dapchi da ta yi saura a hannun yan Boko Haram, Rebecca Sharibu ta isa Landan domin ganawa da Firaminista kan lamarin yarta

- Misis Rebecca Sharibu ta yi zargin cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari bai damu da lbatun ceto yarta ba

- Ta kuma ce za ta kai kukanta ga Firaministan Birtaniya don tilastawa gwamnatin Najeriya kara himma wajen kubutar da 'yarta

Mahaifiyar Leah Sharibu, yarinyar makarantar Dapchi daya tilo da ta yi saura a hannun yan ta’addan Boko Haram, Rebecca Sharibu ta isa Landan domin ganawa da Firaminista kan lamarin yarta.

Misis Rebecca Sharibu wacce ta yi magana a wata hira da shafin BBC Hausa a Landan ta bayyana cewa, Shugaban kasa Muhammadu Buhari bai damu da lbatun ceto yarta ba.

Sannan ta bayyana cewa, ta je Landan ne domin neman taimakon gwamnatin Birtaniya wajeen ceto Leah daga hannun yan ta’addan.

Mahaifiyar Leah Sharibu ta yi wa Landan tsinke don ganawa da Firaministan Birtaniya
Mahaifiyar Leah Sharibu ta yi wa Landan tsinke don ganawa da Firaministan Birtaniya
Asali: Depositphotos

A cewar Misis Sharibu, shugaba Buhari bai tuntubi iyalansu ba sai watanni bakwai bayan sace ‘yarsu.

Ta kuma yi korafin cewa, bayan Shugaban kasar ya tuntube ta, da kuma turo ministoci uku, inda ya bayar da tabbacin cewa za a saki Leah bad a jimawa ba, tun lokacin Shugaban kasar bai kara ce mata komai ba.

Ta kuma ce za ta kai kukanta ga Firaministan Birtaniya don tilastawa gwamnatin Najeriya kara himma wajen kubutar da 'yarta.

KU KARANTA KUMA: Jami’an tsaro sun samo tarin makamai daga dajin Bauchi

Ta ce: “Tun da aka dauke su a watan Fabrairu amma sai watan bakwai na yi magana da Buhari ya ce Leah za ta dawo ba da dadewa ba kuma bayan sati biyu ya kara turo ministocinsa guda uku suka jaddada alkawalinsa.

"Sun karfafa min guiwa, amma daga waccan rana ban sake jin komi daga gwamnati ba.

"Damuwa na kawai su yi kokari su fitar min da yarinyana. Mu 'yarmu muke so.

"Ina jin ba dadi amma yaya zan yi tun da karfi na ba zai iya ba, kuma gwamnati ba ta yi komi ba.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel