Buhari ya rantsar da shugabannin hukumar da ke kula da Majalisa a Najeriya
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da sabuwar hukumar da ke kula da majalisar dokokin tarayya
- Injiniya Ahmed Kadi Amshi ne sabon shugaban hukumar majalisar dokokin tarayyar
- An sanar da hakan ne a ranar Laraba, 26 ga watan Fabrairu a yayin rantsar da hukumar a fadar shugaban kasa Abuja
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da Injiniya Ahmed Kadi Amshi a matsayin shugaba hukumar da ke kula da majalisar dokokin tarayya, sannan ya kuma kaddamar da wasu 11 a matsayin mambobin hukumar.
An gudanar da taron wanda ya samu halartan Shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan da kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila a zauren fadar Shugaban kasa da ke Abuja.
Taron wanda aka fara da misalin 10:30 na safe ya gabaci zaman majalisar zartarwa na mako wanda aka farad a karfe 11:00 na safe.
KU KARANTA KUMA: Hukumar PPPRA ta fatattaki Ma'aikata saboda ta dauki ‘Ya ‘yan Mala’au aiki
A wani labari na daban, mun ji cewa kudirin da ke kokarin kare shugabannin majalisar tarayya daga bincike, ya tsallake matakin farki a Najeriya.
Wannan kudiri da Honarabul Odebunmi Olusegun ya gabatar ya na yunkurin yi wa sashe na 308 na kundin tsarin mulkin Najeriya wasu ‘yan garambawul.
Idan har an yi nasarar amincewa da wannan kudiri, za ayi wa dokar kasa kwaskwarima ta yadda zai zama ba za a iya binciken shugaban majalisar tarayya ba.
‘Dan majalisar mai wakiltar Yankin jihar Oyo, Odebunmi Olusegun, ya ce ya kawo wannan kudiri ne domin shugabannin majalisa su iya yin aikinsu da kyau.
A cewar Odebunmi Olusegun, idan har aka yi na’am da wannan kudiri, shugabannin majalisar tarayya za su ji dadin aiki ba tare da yin wani rangwame ba.
Shugaban masu rinjaye a majalisar wakilan tarayya, Honarabul Alhassan Ado Doguwa, ya tofa albarkacin bakinsa a lokacin da aka gabatar da kudirin a jiya.
Doguwa ya ce Kakakin majalisa ba ya bukatar kariyar a karon-kansa, sai dai don a tsare majalisa.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.
Asali: Legit.ng