Hayatudeen: "Matakin da Zan Dauka kan 'Yan Bindiga idan na Zama Shugaban kasa"

Hayatudeen: "Matakin da Zan Dauka kan 'Yan Bindiga idan na Zama Shugaban kasa"

  • Mai neman takarar shugaban ƙasa a ADC, Mohammed Hayatudeen, ya ce zai ayyana ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane a matsayin ‘yan ta’adda
  • Hayatudeen ya yi alƙawarin cewa idan har ya ci zabe a 2027, gwamnatinsa za ta ɗauki matakin murƙushe duk wata ƙungiyar masu aikata laifuffuka
  • Tsohon masanin tattalin arzikin ya ce rashin tsaro ya zama babbar barazana ga zaman lafiya, tattalin arziki da haɗin kan Najeriya a matsayin kasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Mai neman takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar ADC, Mohammed Hayatudeen, ya sha alwashin ayyana ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane a matsayin ƙungiyoyin ta’addanci idan ya zama shugaban Najeriya a 2027.

Hayatudeen ya bayyana hakan ne yayin wani taron tattaunawa da mutanen gari da aka shirya masa mai suna wanda ƙungiyar Team Rebuild ta gudanar a Abuja ranar Juma’a.

Kara karanta wannan

2027: Tsohon shugaban a INEC ya samu tikiti, zai tsaya takarar gwamnan Yobe a ADC

Mohammed Hayatudeen ya ce zai ayyana 'yan bindiga da masu garkuwa da mutane matsayin 'yan ta'adda.
Mohammed Hayatudeen rike da fom din neman tsayawa takara na ADC Hoto: @ADCVanguard
Source: Facebook

“Ba za mu ci gaba da rayuwa cikin tsoro ba”

Tsohon ma’aikacin bankin kuma masanin tattalin arzikin ya ce Najeriya ba za ta iya ci gaba da jure matsalar rashin tsaro da ayyukan ta’addanci ba, in ji rahoton Punch.

A cewarsa, gwamnatinsa za ta ɗauki matakin murƙushe masu aikata laifuffuka tun daga ranar farko da zai hau mulki.

“Lokaci ya yi da Najeriya za ta daina ɗaukar tsoro, rashin doka da aikata laifi a matsayin wani abu na yau da kullum,” in ji Hayatudeen.

Hayatudeen ya bayyana cewa za a gurfanar da duk wani ɗan bindiga ko mai garkuwa da mutane ƙarƙashin dokar yaƙi da ta’addanci.

Ya jaddada cewa:

“Tun daga ranar farko ta mulkina, za mu ayyana ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane a matsayin ‘yan ta’adda."

Ya ƙara da cewa za a gano kadarorin mutanen da ke ɗaukar nauyin ayyukan ta’addanci tare da kwace su.

Kara karanta wannan

Hankalin Wike ya tashi da gwamnan Oyo ya fito zai kara da Tinubu a 2027

Za a dakatar da tattaunawa da ‘yan bindiga

Ɗan siyasar ya kuma ce lokaci ya yi da gwamnati za ta daina ci gaba da tattaunawa mara iyaka da ƙungiyoyin masu aikata laifuffuka.

A cewarsa, ci gaba da yin sulhu da masu tayar da kayar baya yana ƙarfafa su ne maimakon rage ayyukansu, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

A cikin shekaru da suka gabata, Najeriya ta fuskanci ƙaruwar hare-haren ‘yan bindiga, satar mutane, ta’addanci da rikice-rikicen ƙabilanci musamman a yankunan Arewa maso Yamma, Arewa ta Tsakiya da Arewa maso Gabas.

Dubban mutane sun rasa matsugunansu yayin da makarantu, gonaki, manyan hanyoyi da ƙauyuka ke ci gaba da fuskantar hare-hare daga masu aikata laifuka.

Mohammed Hayatudeen ya ce zai tabbatar gwamnatinsa ta murkushe 'yan ta'addan Najeriya.
Mohammed Hayatudeen, masanin kudi kuma mai neman takarar shugabancin Najeriya a ADC. Hoto: Mohammed Hayatudeen
Source: UGC

An soki gwamnati kan matsalar tsaro

Masana harkokin tsaro da ƙungiyoyin farar hula sun sha sukar yadda gwamnatin tarayya ke tunkarar matsalar rashin tsaro.

Hayatudeen ya ce rashin tsaro ya zama babbar barazana ga wanzuwar Najeriya, tattalin arziki da haɗin kan ƙasa.

Ya bayyana matsalar a matsayin wata babbar masifa da kuma alamar gazawar shugabanci.

Kara karanta wannan

Tsohon mataimakin gwamna ya samu tikitin takara, zai kara da Gwamnan Sokoto

A cewarsa, ba za a samu ci gaban tattalin arziki mai ma’ana ba a ƙasar da mutane ba sa iya zirga-zirga ko saka hannun jari cikin kwanciyar hankali.

Hayatu-Deen ya sayi fom din takara a ADC

Tun da fari, mun ruwaito cewa, an samu wanda ya fara sayen fom din neman takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam'iyyar ADC a zaben 2027.

Mohammed Hayatu-Deen ya yi alƙawarin magance matsalar rashin tsaro, samar da ayyukan yi, da kuma sauƙaƙa tsadar rayuwa da miliyoyin ’yan Najeriya ke fuskanta.

Mohammed Hayatu-Deen, wanda shahararren masanin tattalin arziki ne, shi ne mai neman takara na farko da ya karɓi fom ɗin takarar shugaban ƙasa na ADC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com