Yanzu Yanzu: An dakatar da hadimin Obaseki daga APC

Yanzu Yanzu: An dakatar da hadimin Obaseki daga APC

- Jam’iyyar APC ta dakatar da hadimin gwamnan jahar Edo, Kaycee Osamwonyi

- Shugabanni jam’iyyar mai mulki na yankinsa ne suka dakatar dashi

- An dakatar da hadimin gwamnan ne kan zargin aikata ayyukan da ya kawo tozarci ga jam’iyyar

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta dakatar da Kaycee Osamwonyi, hadimin gwamnan jahar Edo, Godwin Obaseki daga jam’iyyar mai mulki kan zargin aikata ta’addanci da kawo rabuwar kai a jam’iyyar mai mulki.

A cewar jaridar The Nation, shugabannin APC na unguwa shida karamar hukumar Uhunmwode ne suka dakatar da Osamwonyi. Hon. Harrison Otobor ne ya gabatar da batun dakatarwar nasa sannan ya samu goyon bayan mambobin jam’iyyar da ke a taron.

Yanzu Yanzu: An dakatar da hadimin Obaseki daga APC
Yanzu Yanzu: An dakatar da hadimin Obaseki daga APC
Asali: UGC

An kuma tattaro cewa jam’iyyar ta dakatar da Osamwonyi ne saboda kasancewa da hannu a wasu lamura da suka kawo tozarci ga APC, wanda ya saba ma kundin tsarin jam’iyyar.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya rantsar da shugabannin hukumar da ke kula da Majalisa a Najeriya

Biyo bayan zarge-zargen a kan Kaycee, sai aka kafa wani kwamitin ladabtarwa domin ta yi duba zuwa ga lamarin sannan ta gabatar da rahoton binciken ta cikin makonni biyu.

A wani labarin kuma, mun ji cewa kotun koli tayi watsi da bukatar jam'iyyar APC na kara duba shari'ar kwace kujerar gwamnan jihar Bayelsa daga David Lyon da mataimakinsa a jam'iyyar APC.

Kamar yadda mai shari'a Amina Augie ta karanto hukuncin a ranar Laraba, ta bayyana cewa bukatar ba ta da makama kuma hukuncin kotun shi ne madaidaici kuma na karshe.

Ta kara da cewa masu mika bukatar sun kasa bayyana kuskuren, don haka hukuncin ne na karshe a ko ina.

Alkalin kotun kolin ta ce hukuncin ne na karshe kuma babu wata kotu a duniya da za ta iya sauya hukuncin.

Ta kara da cewa wannan bukatar ba ta da amfani kuma wanda ya shigar da wannan bukatar zai biya tarar naira miliyan 10.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng