Gwamna Zulum Ya ba da Mamaki, Ya Ki Tsayawa Takarar Sanata a 2027
- Gwamna Babagana Umara Zulum ya ce ba zai tsaya takarar kujerar Sanata ba bayan kammala wa’adinsa na shekara takwas a Borno
- Ya yi magana yana mai bayyana cewa hankalinsa ya karkata ne wajen tabbatar da zaman lafiya da haɗin kai a tsarin zaɓen fitar da gwani
- Zulum ya bayyana hakan ne yayin taron masu ruwa da tsaki a Maiduguri, inda ya buƙaci masu neman takara su bi doka da oda
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Borno - Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya ce ya ƙi yarda da matsin lamba daga magoya baya da abokai da ‘yan uwa na ya tsaya takarar kujerar Sanata a babban zaɓen 2027.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da yake jagorantar taron manyan masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC a jihar Borno a Maiduguri, gabanin zaɓen fidda gwani.

Kara karanta wannan
"Ba dai a matsayin rauni ba," Gwamna Radda ya kafa sharadin sulhu da 'yan bindiga

Source: Facebook
Legit ta tattaro bayanan da Farfesa Babagana Zulum ya yi ne a wani sako da mai magana da yawunsa, Dauda Iliya ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Zulum ba zai yi takara ba
Rahoton da jaridar Daily Trust ta wallafa ya nuna cewa gwamna Babagana Zulum ya sanar da cewa an matsa masa lamba ya nemi Sanata amma ya ki amincewa.
Gwamnan ya ce:
“Duk da irin matsin lambar da magoya baya da mutanen da ke kusa da ni suka yi, na zaɓi haɗin kai da daidaiton jam’iyya fiye da burina na kaina.
Farfesa Zulum ya kara da cewa:
"Na gaya musu cewa ba zan nemi kujerar Sanata ba domin a ci gaba da kyakkyawar alaƙa,"
Magana kan sulhu a Borno
Zulum, wanda ya nemi a yi ƙoƙarin ƙarshe na cimma matsaya maimakon zaɓen fidda gwani kai-tsaye tsakanin masu neman takara da za su fafata, ya buƙace su da su yi koyi da shi.
Gwamnan aa kuma shawarci jam’iyyar da ta yi zaɓen fidda gwani idan masu neman takara suka yi watsi da tsarin yarjejeniya
“A matsayina na ɗan dimokuraɗiyya, ba zan tilasta wa wata mazaɓa wani ɗan takara ba, sai dai in ƙarfafa mu ci gaba da tuntubar masu ruwa da tsaki domin samar da ‘yan takara ta hanyar sulhu,”
In ji Zulum.

Source: Facebook
Taron, wanda ya samu halartar dukkan manyan masu ruwa da tsaki na jam’iyyar, ya kara kaimi kan yin ƙoƙarin cimma matsaya domin hana ɓaraka a APC.
Malami ya rasa takara a Sokoto
A wani labarin, mun kawo muku cewa malamin addinin Musulunci, Sheikh Bashir Ahmad Sani Sokoto ya rasa takarar gwamna a Sokoto a ADC.
Malamin ya bayyana cewa ya fito neman takara ne domin ceto talakawan jihar Sokoto daga kuncin rayuwa amma Allah bai sa hakan zai yiwu a yanzu ba.
Ya bukaci magoya bayan shi daga ko ina da su cigaba da kasancewa tare da shi, yana mai cewa kada su cire tsammani daga samun nasara.
Asali: Legit.ng
