Gwamnatin Tinubu Ta Kulla Sabuwar Yarjejeniya da Jamus, Za a Kashe €65m a Najeriya

Gwamnatin Tinubu Ta Kulla Sabuwar Yarjejeniya da Jamus, Za a Kashe €65m a Najeriya

  • Najeriya da Jamus sun ƙarfafa alaƙarsu ta tattalin arziki da sababbin yarjejeniyoyi kan makamashi, noma, fasahar zamani da bunkasa matasa
  • Gwamnatin Jamus ta amince da bayar da tallafin kusan euro miliyan 65 domin ayyukan ci gaba a Najeriya
  • Kasashen biyu sun tattauna kan shirin horar da matasan Najeriya miliyan ɗaya dabarun fasaha da na zamani domin samar da ayyukan yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Kasashen Najeriya da Jamus sun sake jaddada aniyarsu ta ƙarfafa haɗin gwiwar tattalin arziki da ci gaba ta hanyar sababbin yarjejeniyoyi da suka shafi zuba jari, noma, makamashi, ilimi da fasahar zamani.

An cimma wannan matsaya ne yayin wata ganawa ta manyan jami’an kasashen biyu a Abuja, inda suka rattaba hannu kan yarjejeniyar ci gaba da haɗin gwiwa tare da duba ayyukan da ake gudanarwa a yanzu.

Kara karanta wannan

Mai son takarar gwamna ya yi gargadin tarwatsewar APC a Taraba

Najeriya da Jamus sun kulla sabuwar yarjejeniyar bunkasa tattalin arziki.
Ministocin Najeriya kan kasafi da tattalin arziki, Abubakar Bagudu (dama), Dr Doris Uzoka-Anite (hagu) tare da wakilin Jamus, Mr Philip Knill (tsakiya). Hoto: @BolajiAdebiyi2
Source: Twitter

Ministan Tinubu ya yabawa gwamnatin Jamus

Ministan kasafin kuɗi da tsare-tsaren tattalin arziki, Sanata Abubakar Atiku Bagudu, ya bayyana cewa wannan haɗin gwiwa wata muhimmiyar nasara ce a dangantakar Najeriya da Jamus, in ji rahoton Arise News.

Ya ce yarjejeniyar ta nuna yadda kasashen biyu ke aiki tare bisa mutunta juna, ci gaba mai ɗorewa da bunkasa tattalin arzikin al’umma.

Bagudu ya gode wa gwamnatin Jamus da hukumominta irin su BMZ, KfW Development Bank da GIZ saboda irin goyon bayan da suke bai wa Najeriya.

Jamus za ta bayar da euro miliyan 65

Daya daga cikin manyan abubuwan da aka cimma shi ne amincewar Jamus na bayar da kusan euro miliyan 65 domin ayyukan haɗin gwiwa a fannoni daban-daban.

Haka kuma kasashen biyu sun tattauna kan wani tsarin bada lamunin euro miliyan 300 domin jawo hankalin masu zuba jari masu zaman kansu da kuma tallafawa manyan ayyukan raya kasa a Najeriya.

Kara karanta wannan

An ware Naira Biliyan 1.4 domin saya wa Gwamna Ahmed Aliyu sababbin motocin aiki

Sabuwar yarjejeniyar ta fi mayar da hankali kan bunkasa noma, sauyin makamashi, horar da matasa, inganta harkar lafiya da kuma bunkasa tattalin arziki.

Ayyukan kamfanonin Jamus a Najeriya

Kamfanonin Jamus irin su Siemens da SAP sun nuna irin ayyukan da suke yi a Najeriya musamman a bangaren makamashi da fasahar zamani.

Kamfanin Siemens ya bayyana yadda yake taimakawa wajen horar da ma’aikatan bangaren lantarki da kuma ayyukan samar da wutar lantarki.

SAP kuma ya gabatar da hanyoyin zamani da za su taimaka wajen inganta tsarin haraji da tsarin tafiyar da gwamnati ta hanyar fasahar zamani, in ji rahoton Vanguard.

Najeriya da Jamus sun kulla sabuwar yarjejeniyar bunkasa tattalin arziki.
Ma'aikatar kasafin Najeriya da gwamnatin Jamus sun rattaba hannu kan sababbin yarjejeniyoyi a ofishin jakadancin Jamus, Abuja. Hoto: @BolajiAdebiyi2
Source: Twitter

Shirin horar da matasa miliyan ɗaya

Tawagar Jamus karkashin jagorancin Philip Knill daga BMZ ta bayyana aniyar taimakawa wajen horar da matasa ‘yan Najeriya har miliyan ɗaya.

An ce za a koya musu dabarun sana’o’i, fasahar AI da ilimin zamani domin samar musu da ayyukan yi da bunkasa tattalin arziki.

Jamus ta yabawa sauye-sauyen tattalin arzikin da gwamnatin Bola Tinubu ke aiwatarwa karkashin shirin Renewed Hope Agenda.

Kasar Jamus ta shiga wasu kauyukan Najeriya

Kara karanta wannan

Bayan tadiye yaransa a tantancewar APC, Fubara ya magantu kan alakarsa da jam'iyya

A wani labari, mun ruwaito cewa, wani wakilin gwamnatin kasar Jamus ya shiga wasu kauyukan Najeriya domin duba wadanda aka kai wa hare-hare.

Thomas Rachel ya shiga wasu yankunan jihar Benue tare da alkawarin cewa suna shirye wajen tallafawa Najeriya ta magance rashin tsaro.

Gwamnatin jihar Benue ta yaba wa Thomas Rachel bisa zuwa wuraren da aka kai hari tare da cewa tana shirye domin daukar mataki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com