Soyayya ce ta jani, shi kuma saurayina ya koya mini garkuwa da mutane - Cewar Hassana

Soyayya ce ta jani, shi kuma saurayina ya koya mini garkuwa da mutane - Cewar Hassana

- Yan sanda a jahar Niger sun kama wata mata ‘yar shekara 32 wacce aka ambata da suna Hassana Bala kan yunkurin yin garkuwa da wani mutum dan shekara 23

- Lamarin ya afku ne a kauyen Kawo a karamar hukumar Kontagora da ke jahar ta Niger

- Hassana ta ce saurayinta ne ya koyar da ita wannan mummunan dabi'a ta garkuwa da mutane

Rundunar yan sanda a jahar Niger ta kama wata mata ‘yar shekara 32 wacce aka ambata da suna Hassana Bala kan yunkurin yin garkuwa da wani mutum dan shekara 23, Umar Sarkin Turaku na kauyen Kawo a karamar hukumar Kontagora da ke jahar.

Hassana ta tura kiran barazana zuwa ga wayar Turaki inda ta nemi ya biya fansar kudi naira miliyan biyar ko kuma ayi garkuwa da shi.

Sai dai abun ya cika da ita matar wacce ke da yara biyu, lokacin da Turaki ya kai rahoton kiran da ake masa ga yan sanda wadanda suka bi diddigi suka gano Hassana sannan suka kama ta.

Soyayya ce ta jani, shi kuma saurayina ya koya mini garkuwa da mutane - Cewar Hassana
Soyayya ce ta jani, shi kuma saurayina ya koya mini garkuwa da mutane - Cewar Hassana
Asali: Instagram

Da ta ke zantawa da manema labarai a lokacin da aka gurfanar da ita a Minna, Hassana ta bayyana cewa saurayinta ne ya koyar da ita aikin garkuwa da mutane, inda ta kara da cewa rawar ganin ita take takawa shine yin barazana ga mutane a waya da kuma shirya kudin da za a ajiye yayinda sauran tawagarta ke dauko kudin.

Ta ce: “bayan na rabu da mijina, na samu aboki namiji wanda ya koyar dani wannan mummunan aiki kuma ta hakan ne na fara sana’ar garkuwa da mutane.

KU KARANTA KUMA: Innalillahi: Ana tilasta dalibai mata suna tsirara ana duba tsiraicinsu don a tabbatar da basa al'ada

“Tun bayan da na rabu da mijina rayuwata ta sauya inda ta dada tabarbarewa,” in ji ta, sannan ta nemi a yi mata afuwa.

Kakakin hukumar yan sandan jahar, Muhammad Abubakar ya bayyana cewa za a shigar da lamarin kotu bayan kammala bincike.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng