Ayyukan Oshiomhole ya kawo tozarci ga jam’iyyar APC - Obaseki

Ayyukan Oshiomhole ya kawo tozarci ga jam’iyyar APC - Obaseki

- Gwamna Godwin Obaseki na jahar Edo ya caccaki shugaban jam'iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole

- Obaseki ya bayyana cewa barna da hayaniyar Oshiomhole ya haddasa tozarci da danasani a jam’iyyar mai mulki

- Gwamnan ya ce sakacin Oshiomhole a kan jam’iyyar da yin yadda ya ga daman na ci gaba da kawo wa APC asara

Gwamnan jahar Edo, Godwin Obaseki, ya bayyana cewa barna da hayaniyar Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Adams Oshiomhole ya haddasa tozarci da danasani a jam’iyyar mai mulki.

A wani jawabi daga hadiminsa, Crusoe Osagie, gwamnan ya ce sakacin Oshiomhole a kan jam’iyyar da yin yadda ya ga daman na ci gaba da kawo wa APC asara, wanda na baya-bayan nan shine hukuncin kotun koli kan bukatar sake duba zaben gwamnan bBayelsa wacce jam’iyyar da dan takararta na gwamna, David Lyon suka yi.

Ayyukan Oshiomhole ya kawo tozarci ga jam’iyyar APC - Obaseki
Ayyukan Oshiomhole ya kawo tozarci ga jam’iyyar APC - Obaseki
Asali: UGC

“Mun lura da yadda ayyukan dakataccen Shugaban jam’iyyar APC na kasa na baya-bayan nan, wanda sakacinsa da hayaniyarsa ke ci gaba da kawowa jam’iyyar tarin asara da tozarci.

“Misali, abun bakin ciki ne cewa Oshiomhole ya tozarta yan Najeriya maganganunsa na son zuciya bayan hukuncin kotun koli kan zaben Bayelsa, inda ya bayyana hukuncin a matsayin rashin aldalci.

“Sai kace wannan bai isa ba, ya kuma caccaki hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) kan bin umurnin kotun koli da ta yi, inda ya yi barazanar janye hukuncin, wanda duk wani dan Najeriya mai tunani ya san shine na karshe,” in ji shi.

KU KARANTA KUMA: Za’a tura tubabbun mayakan Boko Haram jami’o’in kasashen waje don yin karatu

Ya ce abun bakin ciki ne cewa bayan kwamitin masu ruwa da tsaki da Oshiomhole ke jagoranta ya ki yin aikin sa kan zabar yan takara a zaben gwamnan Nuwamba da aka yi a Bayelsa, ya kuma bata sunan jam’iyyar tare da tozarta babbar kotun kasar da kwamitin Mambobin jam’iyyar APC.

A wani labari na daban, mun ji cewa Jami'an rundunar 'yan sandan Najeriya, a ranar Alhamis sun dakile afkuwar kazamin rikici tsakanin 'yan jam'iyyar All Progressives Congress (APC) masu goyon bayan shugaban jam'iyyar Adams Oshiomhole da wadanda ba su goyon bayan sa a sakatariyar jama'iyyar da ke birnin tarayya Abuja kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng