Gwamnan Zamfara ya tursasa shugabannin makarantun kwana cin irin abincin da suke ciyar da dalibai

Gwamnan Zamfara ya tursasa shugabannin makarantun kwana cin irin abincin da suke ciyar da dalibai

- Gwamna Bello Matawalle ya bukaci shugabannin makarantun sakandare da jami’an da ke ciyar da dalibai a jahar da su dunga ci daga cikin abincin da suke ciyar da daliban makarantun kwana ko kuma a sallame su

- Hakan ya biyo bayan ziyarar bazata da Matawalle ya kai makarantun kwana na gwamnati a jahar, sannan ya ga irin abincin da ake ciyar da daliban

- Ana dai ciyar da yaran ne da abinci mara inganci da tsafta

Gwamnan jahar Zamfara, Dr Bello Mohammed Matawalle ya bukaci shugabannin makarantun sakandare da jami’an da ke ciyar da dalibai a jahar da su dunga ci daga cikin abincin da suke ciyar da daliban makarantun kwana ko kuma a sallame su.

Matawalle a yayin wani ziyarar bazata na kwanaki biyu da ya kai makarantun sakandare na kwana ta jahar, wadanda suka hada da Government Science Secondary School, Gusau da Government Girls School, Gusau ya nuna rashin jin dadi kan irin abincin da ake ciyar da dalibai cikin rashin tsafta da karancin inganci.

“Wajibi ne daga yanzu ku duna cin irin abincin da kuke ba daliban ku kuma zan sa a sanya muku idanu sosai saboda duk wanda ya saba ma wannan umurni na cin irin abincin dalibai za a sallame shi,” ya yi gargadi.

Matawalle ya ce abun haushi ne ganin cewa ana ciyar da daliban makarantun kwana abinci mara kyawu duk da makudan kudaden da gwamnati ke kashe wa a shirin ciyarwa.

Gwamnan ya yi gargadin cewa gwamnati ba za ta sake lamuntan irin wannan hali ba sannan cewa daga yanzu za ta yi maganin wadanda ta samu da hannu a aikin da baya bisa ka’ida na dafa abinci mara inganci ga daliban makaranta a jahar.

KU KARANTA KUMA: Mahaifiyar Leah Sharibu ta yi wa Landan tsinke don ganawa da Firaministan Birtaniya

“Daga yanzu, shugabannin makarantun, jami’an ciyarwa da sauran jami’ai a fadin jahar sai sun dunga cin abinci iri guda da suka dafa ma daliban ko a kore su,” ya yi umurni.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel