Aisha Khalid
4688 articles published since 22 Agu 2019
4688 articles published since 22 Agu 2019
Direbobin motocin haya, masu zuwa Abuja zuwa Kaduna sun koka, akan yadda fasinjoji suka gwammaci bin jirgin kasa akan motoci, saboda tsoron fadawa 'yan bindiga.
Sifeta janar na 'yan sanda, Mohammed Adamu, yace babbar matsalar da jami'an tsaro suke fuskanta wurin yin aiki shine yadda 'yan Najeriya su ka yanke tsammani.
A daren Talata ne wasu bata-gari da ba a san ko su wanene ba, suka fasa ofishin babban Alkalin kotun Dogarawa, Mai Shari'a Kabir Dabo da ke Sabon Gari Zaria.
Sauraron shari'ar shugaban kungiyar Shi'a, (IMN), Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da matarsa Zinat, zai cigaba a babbar kotun shari'a ta birnin Kaduna a yau Laraba.
Rundunar sojin kasa tare da na sama karkashin Operation Thunder Strike sun halaka 'yan bindiga masu tarin yawa a wani sansaninsu da ke Kuku a Kagarko da Kaduna.
Fadar shugaban kasa ta musanta zargin da yaketa yawo akan cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya tsani 'yan kabilar Ibo kuma bai yarda da baiwa mata dama ba a harkar.
'Yan bindiga sun cigaba da kai hare-hare kananun hukumomi da ke karkashin jihar Kaduna, kamar Kajuru, Igabi, Giwa da Zangon Kataf, inda suka kashe mutane 16.
Gwamnan jihar Niger, Abubakar Sani Bello, yace yayi amfani da makonni 2 da aka kebesa akan cutar COVID-19, wurin neman gafara wurin Ubangiji, Daily Trust tace.
Kakakin jam'iyyar APC ta jihar Ebonyi, Chika Nwoba, yayi murabus daga kujerarsa. Ya ce ba zai iya zama inuwa daya da Gwamna Umahi na jihar Ebonyi ba a APC.
Aisha Khalid
Samu kari