Na dinga hailala da istigfari a yayin da nake killace sakamakon korona, Gwamnan Niger
- Kebewata ta koyamin darasi, na tabbatar cutar COVID-19 gaskiya ce, cewar gwamnan jihar Niger
- Gwamnan jihar Niger, Abubakar Sani Bello, ya ce yayi amfani da killacewarsa wurin neman gafarar Allah
- Ya fadi hakan ne a ranar Talata, bayan ya dawo daga killacewar, har yayi taro da 'yan majalisar jiharsa
Gwamnan jihar Niger, Abubakar Sani Bello, ya ce yayi amfani da makonni 2 da aka kebesa a kan cutar COVID-19, wurin neman gafara wurin Ubangiji, Daily Trust tace.
Gwamna Bello ya sanar a shafinsa na Twitter, kwanaki 8 da suka gabata, cewa an auna sa, kuma an gane yana dauke da cutar COVID-19, kuma har ya riga ya killace kansa kamar yadda dokar cutar ta tanada.
KU KARANTA: Duba kyaututtuka 30 da budurwa ta gwangwaje saurayinta da shi a ranar zagayowar haihuwarsa
Gwamnan ya kammala kwanakin killace kansa a ranar Talata, har ya kai ziyara majalisar jiharsa.
A cewarsa, "A cikin makonni 2 da na killace kaina na koyi darasi, domin na tabbatar da cewa cutar COVID-19 gaskiya ce. Ya kamata kowa ya kula kuma ya kiyaye dokokin kare kai daga cutar COVID-19."
"Na yi amfani da makonni 2 da na killace kaina wurin neman gafarar mahalicci na. Ya kamata mu kula, kada mu shafawa iyalanmu cutar," cewar gwamnan.
Bello ya yi a kalla sa'a daya tare da 'yan majalisar jiharsa, a wani taron sirri, ya sanar da manema labarai cewa yayi godiya ga 'yan majalisarsa, musamman wadanda suka nuna kauna da damuwa a garesa lokacin da yake killace.
KU KARANTA: Hotunan auren dole da aka yi wa yarinya mai shekaru 13 da dattijo mai shekaru 48
Ya kuma yi godiya akan yadda aka mika kasafin 2021, kuma sun tattauna akan cigaban jihar.
A wani labari na daban, rundunar sojin sama ta Operation LAFIYA DOLE, ta ragargaji 'yan Boko Haram a dajin Sambisa da ke jihar Borno, jaridar Leadership ta wallafa.
Kakakin rundunar sojin, Manjo Janar John Enenche, ya ce rundunar ta yi harbin ne ta sama, a bangarori 2, bangaren Sambisa da Gobara, inda yace sun yi amfani da salo na musamman don kai wa 'yan Boko Haram din hari.
Ya ce sojojin sun yi harbin ne daidai wuraren da suke zargi. Saboda sai da suka duba kuma suka yi nazari a wuraren da 'yan ta'addan suka kafa daba, tukunna suka yi harbin. Hakan ya yi sanadiyyar kashe yawancinsu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng