Hare-haren 'yan bindiga ya salwantar da rayuka 16 a kananan hukumomi 4 na Kaduna

Hare-haren 'yan bindiga ya salwantar da rayuka 16 a kananan hukumomi 4 na Kaduna

- Masu garkuwa da mutane suna cigaba da kai hare-hare kauyakun jihar Kaduna

- 'Yan ta'addan sun kai hari Kajuru, Igabi, Giwa da Zangon Kataf ranar Litinin da Talata

- Sakamakon hare-haren, mutane 16 sun rasa rayukansu, sun kuma yi garkuwa da wasu

'Yan bindiga sun cigaba da kai hare-hare kananun hukumomi da ke karkashin jihar Kaduna, kamar Kajuru, Igabi, Giwa da Zangon Kataf, inda suka kashe a kalla mutane 16 a ranar Litinin da Talata.

Sun saci mutane da dama, kuma sun harbi a kalla mutane 4.

Sun kai hari a ranar Lahadi hanyar Kaduna zuwa Abuja har suka yi sanadiyyar mutuwar mutane 15, kuma suka kwashe daliban jami'ar Ahmadu Bello 8.

Gwamnatin jihar Kaduna, ta tabbatar da kisan mutane 11 a kauyen Albasu, da ke karkashin karamar hukumar Igabi, Daily trust ta ruwaito.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan, ya ce wasu mutane 4 sun rasa rayukansu sakamakon raunukan da 'yan ta'addan su ka ji musu.

Jami'an tsaro sun ce an kashe wani Albarka Addu'a, tsohon dagacin kauyen Kyemara Gari a ranar Lahadi, bayan 'yan bindigan sun yi garkuwa da wasu mutane 2 a Maraban Kajuru a karamar hukumar Kajuru.

Ya kuma tabbatar da harin da aka kai kauyakun Fatika, Kaya da Yakawada da ke karkashin karamar hukumar Giwa a ranar Talata, wanda hakan yayi sanadiyyar mutuwar mutane 2, sannan an yi garkuwa da mutane da dama.

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Mayakan Boko Haram sun harbo jirgin sama a Borno

Hare-haren 'yan bindiga ya salwantar da rayuka 16 a kananan humumomi 4 na Kaduna
Hare-haren 'yan bindiga ya salwantar da rayuka 16 a kananan humumomi 4 na Kaduna. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Duba kyaututtuka 30 da budurwa ta gwangwaje saurayinta da shi a ranar zagayowar haihuwarsa

A wani labari na daban, rundunar sojin sama ta Operation LAFIYA DOLE, ta ragargaji 'yan Boko Haram a dajin Sambisa da ke jihar Borno, jaridar Leadership ta wallafa.

Kakakin rundunar sojin, Manjo Janar John Enenche, ya ce rundunar ta yi harbin ne ta sama, a bangarori 2, bangaren Sambisa da Gobara, inda yace sun yi amfani da salo na musamman don kai wa 'yan Boko Haram din hari.

Ya ce sojojin sun yi harbin ne daidai wuraren da suke zargi. Saboda sai da suka duba kuma suka yi nazari a wuraren da 'yan ta'addan suka kafa daba, tukunna suka yi harbin. Hakan ya yi sanadiyyar kashe yawancinsu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel