Jigo a APC ya yi murabus, ya ce ba zai iya zama inuwa daya da Umahi ba

Jigo a APC ya yi murabus, ya ce ba zai iya zama inuwa daya da Umahi ba

- Kakakin jam'iyyar APC na jihar Ebonyi, Chika Nwobi, ya yi murabus

- Ya rubuta hakan a wata takarda, wacce yace ya hakura da kujerar tasa

- A cewarsa, ba zai iya aiki da gwamnan jihar Ebonyi ba, David Umahi

Kakakin jam'iyyar APC na jihar Ebonyi, Chika Nwoba, ya yi murabus daga kujerarsa.

Ya sanar da hakan a wata takarda da ya fitar a ranar Litinin, wacce ya mika godiyarsa ga jam'iyyar APC da shugabannin jam'iyyar, da su ka ga cancantarsa, har su ka zabe sa, suka kuma daura sa a kujerar a 2018, lokacin yana da shekaru 27.

Ya sanar da hakan a wata tattaunawa da jarida Punch tayi da shi ta waya, inda yace zai bar jam'iyyar APC saboda ba zai iya aiki da gwamnan jihar Ebonyi ba, David Umahi.

"Ba zan iya aiki tare da Gwamnan jihar Ebonyi ba, David Umahi," jigon jam'iyyar APC ya sanar yayin maganarsa a kan barin mukaminsa na sakataren yada labarai na APC.

KU KARANTA: Hotunan auren dole da aka yi wa yarinya mai shekaru 13 da dattijo mai shekaru 48

Jigo a APC ya yi murabus, ya ce ba zai iya zama inuwa daya da Umahi ba
Jigo a APC ya yi murabus, ya ce ba zai iya zama inuwa daya da Umahi ba. Hoto daga @MobilePunch
Asali: Twitter

KU KARANTA: Dakarun sojin saman Najeriya sun ragargaza sansanin 'yan Boko Haram a Sambisa

A wani labari na daban, tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo, zai je kasar Ethiopia sasanci. Zai sasanta tsakanin gwamnatin kasar ne da TPLF, duk da gwamnatin ta nuna karara cewa ba ta so a taso da batun.

Kamar yadda labarin ya bayyana, shugaban kasar Uganda, Yoweri Museveni ya yi maganar a shafinsa na Twitter, amma sai ya goge.

Gwamnatin kasar ta ce, jam'iyya mai mulki a Tigray, ta ki amincewa da sasanci tsakaninta da gwamnatin tarayyar tun shekaru 2 da suka wuce.

Kamar yadda ministan harkokin waje na Ethiopia, Redwan Hussain ya sanar da manema labarai a Addis Ababa, ya ce "Duk wani kokarin sasanci zai iya janyo fadace-fadace da tayar da zaune tsaye."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel