Ahmed Makarfi: Tsohon Gwamnan Kaduna Ya Samo Mafita ga Tinubu kan Rashin Tsaro

Ahmed Makarfi: Tsohon Gwamnan Kaduna Ya Samo Mafita ga Tinubu kan Rashin Tsaro

  • Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Ahmed Mohammed Makarfi ya nuna damuwarsa kan matsalar rashin tsaron da ta addabi Najeriya
  • Sanata Ahmed Makarfi ya bayyana cewa rashin shawo kan matsalar rashin taaro na ci gaba da kawo koma baya ga kasar nan
  • Tsohon gwamnan ya bayyana cewa maimaikon ya yi suka kan lamarin, ya gwammace ya ba da shawara kan yadda za a shawo kan matsalar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kaduna - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Ahmed Mohammed Makarfi, ya buƙaci Shugaba Bola Tinubu da ya ayyana dokar ta-ɓaci ta ƙasa a kan matsalar tsaro.

Ahmed Mohammed Makarfi ya yi gargaɗin cewa taɓarɓarewar tsaro da ƙasar ke fuskanta tana buƙatar daukar muhimman matakai da kuma haɗin gwiwar ƙasa baki ɗaya.

Makarfi ya ba Shugaba Tinubu shawara
Ahmed Mohammed Makarfi da shugaban kasa Bola Tinubu Hoto: Ahmed Mohammed Makarfi, Bayo Onanuga
Source: Facebook

Jaridar The Punch ta kawo rahoto cewa tsohon gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin wata tattaunawa da ya yi da manema labarai a gidansa da ke Kaduna ranar Lahadi, 21 ga watan Yunin 2026.

Kara karanta wannan

Janar Abdulsalam ya sanya yada labaran karya cikin abu 2 da ke rura witar rashin tsaro

Ahmad Makarfi ya tabo batutuwa

Makarfi ya yi magana a kan halin da dimokuradiyya ke ciki, rashin tsaro, shirye-shiryen zaɓubbukan 2027, da kuma rikicin da ke cikin jam'iyyar PDP.

Ya ce ko da yake dorewar tafiyar dimokuradiyyar Najeriya ba tare da katsewa ba tun shekarar 1999 babban abin a-zo-a-gani ne, rashin samun nasarar shawo kan matsalar tsaro na ci gaba da raunata shugabanci da ci gaban tattalin arziki.

Me Makarfi ya ce kan rashin tsaro?

A cewarsa, ya kamata a ɗauki batun tsaro a matsayin babban fifiko na ƙasa saboda tasirinsa kai-tsaye ga haɓakar tattalin arziki, daidaiton al'umma, da ci gaban ƙasa, Premier Radio ya kawo labarin.

Makarfi ya bayyana cewa samun gagarumin ci gaba wajen yaƙar rashin tsaro zai inganta harkokin tattalin arziki kai tsaye tare da rage radadin da ake ciki a faɗin ƙasar.

Wace shawara ya ba Shugaba Tinubu?

Yayin da yake magana kan yadda gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ke tunkarar ƙalubalen tsaro, tsohon gwamnan ya ce yin suka kaɗai ba zai magance matsalar ba, inda ya buƙaci shugabanni a dukkan matakai da su mayar da hankali kan mafita ta zahiri.

Kara karanta wannan

APC ta yi magana da 'yan majalisa suka fara maganar Tinubu ya sauka

Makarfi ya ba da shawara kan tsaro
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Ahmed Mohammed Makarfi Hoto: Ahmed Mohammed Makarfi
Source: Facebook
“Gaskiyar magana ita ce, a ƙasa, ƙalubalen tsaro suna ƙara faɗaɗa. Don haka, a gare ni, maimakon yin suka, gara a ba da shawara."
“Ya kamata shugaban kasa, tare da haɗin gwiwar gwamnatocin jihohi, su ayyana dokar ta-ɓaci a kan tsaro. Kamata ya yi tsarin shugabanci ya sauya ta yadda abu na ɗaya, na biyu da na uku da za a ba wa fifiko su kasance harkar tsaro a kowane ɓangare."

- Ahmed Mohammed Makarfi

An yi wa mamar Tinubu addu'a

A wani labarin kuma, kun ji cewa an gudanar da taron addu'o'i da tunawa da mahaifiyar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.

A lokacin da Kashim Shettima yake jawabi a wajen taron, ya ce marigayiyar ta kasance abin koyi a bangaren shugabanci wajen kawo sauyi a rayuwar jama'a.

Ya bayyana ta a matsayin shugaba mai sadaukar da kai kuma har yanzu tana ci gaba da tasiri a Najeriya ta hanyar dabi'u da ta dasa a ɗanta.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng