Shugabancin kasan yankin Ibo a 2023: Babu gudu, babu ja da baya, Sanata Abaribe
- Sanata Enyinnaya Abaribe ya ce ba za su amince ba, matsawar ba a tsayar da Ibo takarar shugaban kasa ba
- Sanatan jihar Abia ya ce za su cigaba da nema wa mutanen kudu maso gabas adalci a kan shugabancin kasar nan
- A cewarsa, a bai wa mutanen yankin damar mulkar Najeriya da zarar Shugaba Buhari ya sauka a shekarar 2023
Sanatan daga jihar Abia, Enyinnaya Abaribe, ya jajirce a kan mulkin dan kabilar Ibo a shekarar 2023.
Ya fadi hakan ne a ranar Laraba, 18 ga watan Nuwamba, lokacin da kungiyar manema labarai na Najeriya, NUJ a jihar Imo suka gayyace shi don bashi jinjina ta musamman a matsayinsa na "Sanatan kudu maso gabas da yafi kowa kwazo a 2020."
Abaribe, wanda yake wakiltar Abia ta kudu, ya lashi takobin kare hakkin yankinsa, don tabbatar musu da adalci.
Shugaban marasa rinjayen, ya ce ba za su yi saurin karaya ba, kuma za su jajirce wurin ganin sun tsaya tsayin daka har sai mafita ta samu, kuma sai sun tabbatar burinsu ya cika.
A cewarsa, wajibi ne a bai wa dan yankinsu damar shugabancin kasa a shekarar 2023, matsawar ana so hankalinsu ya kwanta, kuma su tabbatar ana tare da su, ba wai ana ware su ba.
Jaridar Legit.ng ta ruwaito yadda wani babban lauya, Onyekachi Monday Ubani, ya ce ya kamata a bai wa kudu maso gabas damar maye gurbin Shugaba Muhammadu Buhari.
Ubani, tsohon mataimakin shugaban NBA, wanda dan asalin jihar Abia ne, ya sanar da hakan a wata tattaunawa da aka yi da shi, wacce aka wallafa a ranar Lahadi, 15 ga watan Nuwamba.
Ya ce tun da Najeriya ta amshi mulkin demokradiyya a 1999, dan yankin kudu maso gabas bai hau karagar mulkin Najeriya ba.
Lauyan ya ce ana ta karba-karbar mulkin ne tsakanin Yarabawa, Hausawa, Fulani da 'yan yankin Kudu-kudu.
KU KARANTA: Bidiyon ragargaza sansanin 'Major' da soji suka yi a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja
KU KARANTA: Na dinga hailala da istigfari a yayin da nake killace sakamakon korona, Gwamnan Niger
A wani labari na daban, jam'iyyar PDP tana ta tafka asarar gwamnoni. Yanzu haka, akwai rade-radi kan yadda wani gwamnan PDP ya lashi takobin sauya sheka zuwa APC.
Gwamna Wike ya sanar da hakan a ranar Laraba, 18 ga watan Nuwamba, bayan komawar gwamna David Umahi zuwa jam'iyyar APC.
Kamar yadda ya wallafa a shafinsa na kafar sada zumuntar zamani ta Twitter, inda yace: "Inaso in sanar da ku cewa akwai wani gwamnan PDP da zai bar jam'iyyar, kwanan nan."
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng