An fasa kotun da ake zaman shari'ar Sarkin Zazzau tare da tarwatsa ofishin alkali

An fasa kotun da ake zaman shari'ar Sarkin Zazzau tare da tarwatsa ofishin alkali

- An fasa ofishin babban alkalin kotun da ake shari'ar masarautar Zazzau a Sabon Gari

- Ita ce kotun da ake shari'a tsakanin sabon sarki Ahmed Bamalli da Iyan Zazzau, Bashir Aminu

- A daren talata ne wasu bata-gari suka shiga, inda suka lalata takardun kotun da sauran abubuwa

A daren Talata ne wasu bata-gari da ba a san ko su wanene ba, suka fasa ofishin babban Alkalin kotun Dogarawa, Mai Shari'a Kabir Dabo, wanda yake shari'a tsakanin sabon sarki, Ahmed Bamalli da Iyan Zazzau, Bashir Aminu.

Sai da bata-garin suka fasa kotun, tukunna suka samu damar shiga har ofishin babban alkalin.

Bata-garin sun yi kaca-kaca da wasu takardu, sun kuma kwashe kayan da alkalin yake amfani da su idan zai zauna a kotu, da wasu abubuwa da har yanzu ba a gama tantancewa ba.

Wakilin jaridar Aminiya ya bukaci tattaunawa da magatakardan kotun, mai suna Jafaru, amma abin ya ci tura, inda ya ce yanzu dai ba zai iya magana da shi ba, har sai ya tuntubi mai gidansa.

KU KARANTA: Na dinga hailala da istigfari a yayin da nake killace sakamakon korona, Gwamnan Niger

An fasa kotun da ake zaman shari'ar Sarkin Zazzau tare da tarwatsa ofishin alkali
An fasa kotun da ake zaman shari'ar Sarkin Zazzau tare da tarwatsa ofishin alkali. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Jigo a APC ya yi murabus, ya ce ba zai iya zama inuwa daya da Umahi ba

A wani labari na daban, fadar shugaban kasa ta musanta zargin da yake ta yawo a kan cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya tsani 'yan kabilar Ibo kuma bai yarda da bai wa mata dama ba a harkar mulki.

A ranar Talata, 17 ga watan Nuwamba, Bashir Ahmad, hadimin shugaban kasa a harkar labarai, ya musanta zargin da ake yi wa shugaban kasan.

Ya wallafa a shafinsa na kafar sada zumuntar zamani ta Twitter, inda yace, "Shugaban kasa bai tsani 'yan kabilar Ibo ba. Sannan duk masu yada wannan maganar, su canja salo."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel