Kashe-kashe da garkuwa da mutane: Fasinjoji sun kauracewa hanyar Kaduna zuwa Abuja

Kashe-kashe da garkuwa da mutane: Fasinjoji sun kauracewa hanyar Kaduna zuwa Abuja

- Mutane sun shiga tararrabi a kan bin hanyar Kaduna zuwa Abuja, cewar direbobin motocin haya

- A cewar wani direba, sai su wuni suna jiran fasinjoji, watarana su kan hakura saboda kowa a tsorace yake

- A cewarsa, yanzu mutane sun fi gane wa jirgin kasa, a kan motocin haya saboda tsoron 'yan bindiga

Direbobin motocin haya, masu zuwa Abuja zuwa Kaduna sun koka a kan yadda fasinjoji suka gwammaci bin jirgin kasa a kan motoci, saboda tsoron fadawa hannun 'yan bindiga.

Jaridar Daily trust ta bayyana yadda garkuwa da mutane ya yawaita a wurin 200km na babban titin, cikin 'yan kwanakin nan.

Wani direban garejin Zuba, Abdulsalam Abubakar, wanda kullum cikin bin hanyar Abuja zuwa Kaduna yake, ya ce rashin yawan fasinjojin ya fara ne tun daga lokacin da garkuwa da mutane ya fara zama ruwan dare.

KU KARANTA: Buhari ya so daukar mace daga yankin Ibo a matsayin mataimakiyarsa a 2015, Fadar shugaban kasa

A cewarsa, bayan kudin man fetur ya karu saboda annobar COVID-19, kowa yana fama da kansa, jama'a suka fara baya-baya.

Kashe-kashe da garkuwa da mutane: Fasinjoji sun daina bin hanyar Kaduna zuwa Abuja
Kashe-kashe da garkuwa da mutane: Fasinjoji sun daina bin hanyar Kaduna zuwa Abuja.. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Hare-haren 'yan bindiga ya salwantar da rayuka 16 a kananan hukumomi 4 na Kaduna

"Akwai jami'an tsaro tun daga Zuba zuwa Kaduna, amma fasinjoji basa zuwa saboda tsoro," a cewar Abubakar.

"Sai mutum ya dade sosai yana jiran fasinjoji kafin mota ta cika. Ina fatan jami'an tsaro za su fara kwantar mana da hankali, suna tabbatar mana da tsaron lafiyarmu nan kusa," a cewarsa.

Wani direba, mai suna Bello Murtala, ya ce ya dade sosai a gareji, kafin fasinjoji su cika motar da zai kai su Kaduna, Daily Trust ya wallafa.

A cewarsa, yawan mutanen da ya dauka basu da yawa, idan aka duba yadda da ake turuwa, ana tafiyar wasunsu suna addu'ar Allah ya kaisu lafiya.

Ya ce yanzu haka maimakon N4000, N5000 suke amsa, sannan mutum ba zai samu isassun fasinjoji ba, sun gwammaci su hau jirgin kasa, a kan su bi tituna.

A wani labari na daban, a yau 18 ga watan Nuwamba ake cigaba da sauraron shari'ar El-Zakzaky a Kaduna, kamar yadda gidan talabijin din Channels suka ruwaito.

Dama kotu ta ce za ta cigaba da duban yuwuwar bayar da belin El-Zakzaky wanda ya nema a ranar 5 ga watan Augusta.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel