Da duminsa: A yau Laraba za'a cigaba da shari'ar El-Zakzaky a kotu da ke Kaduna

Da duminsa: A yau Laraba za'a cigaba da shari'ar El-Zakzaky a kotu da ke Kaduna

- A yau, 18 ga watan Nuwamba ne za a cigaba da sauraron shari'ar El-Zakzaky da matarsa

- Idan ba a manta ba, suna hannun hukuma tun watan Disamban 2015, bayan rikicin kungiyar da sojoji

- Dama an dage sauraron shari'ar ne bayan kotu ta ki amincewa da bayar da Belinsa, a ranar 5 ga watan Augusta

A yau 18 ga watan Nuwamba ake cigaba da sauraron shari'ar El-Zakzaky a Kaduna, kamar yadda gidan talabijin din Channels suka ruwaito.

Dama kotu ta ce za ta cigaba da duban yuwuwar bayar da belin El-Zakzaky wanda ya nema a ranar 5 ga watan Augusta.

Sauraron shari'ar shugaban kungiyar Shi'a, (IMN), Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da matarsa Zinat, zai cigaba a babbar kotun shari'a ta birnin Kaduna.

El-Zakzaky da matarsa suna hannun hukuma tun watan Disamban 2015, tun bayan rikicin da ya barke tsakanin kungiyar da sojojin Najeriya a Zaria.

Gwamnatin jihar Kaduna ta zargesu da laifuka 8, ciki har da zargin kashe mutane babu gaira ba dalili, taro ba bisa ka'ida ba da kuma tayar wa da mazauna yankin hankula, da sauran laifuka.

A ranar 29 ga watan Satumba, 2020, shugaban IMN da matarsa sun musanta zargin da ake yi musu, ta bakin lauyansu, Marshall Abubakar, wanda ya wakilci Femi Falana, shugaban lauyoyin.

Ya roki kotu da tayi fatali da kara da zargin da ake yi wa El-Zakzaky.

Mai shari'a, Justice Gideon Kurada ya ki amincewa da wannan bukatar, bayan ya gama sauraron shari'ar.

Ya dage sauraron shari'ar zuwa 18 ga watan Nuwamba da ranar Alhamis, 19 ga watan Nuwamban 2020.

KU KARANTA: Na dinga hailala da istigfari a yayin da nake killace sakamakon korona, Gwamnan Niger

Da duminsa: A yau Laraba za cigaba da shari'ar El-Zakzaky a kotu da ke Kaduna
Da duminsa: A yau Laraba za cigaba da shari'ar El-Zakzaky a kotu da ke Kaduna. Hoto daga @ChannelsTV
Asali: Twitter

KU KARANTA: Kyawawan hotunan tagwaye maza za su aura tagwàye sun janyo cece-kuce

A wani labari na daban, 'yan bindiga sun cigaba da kai hare-hare kananun hukumomi da ke karkashin jihar Kaduna, kamar Kajuru, Igabi, Giwa da Zangon Kataf, inda suka kashe a kalla mutane 16 a ranar Litinin da Talata.

Sun saci mutane da dama, kuma sun harbi a kalla mutane 4. Sun kai hari a ranar Lahadi hanyar Kaduna zuwa Abuja har suka yi sanadiyyar mutuwar mutane 15, kuma suka kwashe daliban jami'ar Ahmadu Bello 8.

Gwamnatin jihar Kaduna, ta tabbatar da kisan mutane 11 a kauyen Albasu, da ke karkashin karamar hukumar Igabi, Daily trust ta ruwaito.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel