Turji Ya Fitar da Sabon Bidiyo, Ya Bayyana yadda Ya Hallaka Sojojin Najeriya

Turji Ya Fitar da Sabon Bidiyo, Ya Bayyana yadda Ya Hallaka Sojojin Najeriya

  • Majiyoyi sun tabbatar da cewa daya daga cikin jagororin ‘yan bindiga, Bello Turji ya fitar da bidiyo a jihar Sokoto
  • An ce fashewar bam ta kashe sojoji biyu tare da jikkata wasu yayin da suke amsa kiran gaggawa bayan harin ‘yan bindiga
  • Wani mai rajin tsaro ya yi zargin cewa mayaƙan Turji na samun sabbin makamai da horo a yankunan kan iyakar Sokoto da Zamfara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Sokoto - Shahararren jagoran ‘yan bindiga, Bello Turji, ya sakeyin magana a wani faifain bidiyo wanda ya yadu a kafofin sadarawa.

Bello Turji ya yi magana bayan kashe wasu sojoji a Sokoto wanda ya sake sanya faragaba a zukatan al'ummar yankin.

Turji ya fitar da sabon bidiyo a Sokoto
Dan ta'adda, Bello Turji da Hafsan tsaron kasa, Janar Olufemi Oluyede. Hoto: HQ Nigerian Army.
Source: Facebook

Legit Hausa ta samu wannan bidiyo ne a shafin malamin Musulunci, Murtala Bello Sokoto wanda ya wallafa a shafin Facebook.

Kara karanta wannan

An ga tashin hankali da bam ya tarwatse da sojoji a Sokoto, an rasa rayuka

Yadda aka hallaka sojoji 2 a Sokoto

Majiyoyi sun ruwaito cewa aƙalla sojoji biyu sun rasa rayukansu yayin da wasu da dama suka jikkata sakamakon fashewar bam a kan motar sojoji.

An ce sojojin na kan hanyarsu ta zuwa ƙauyen Bargaja da ke ƙaramar hukumar Isa bayan samun kiran neman agaji sakamakon harin ‘yan bindiga.

Mazauna yankin sun bayyana cewa ‘yan bindiga sun mamaye ƙauyen tsakanin ƙarfe goma sha biyu da rabi na dare zuwa uku na safiya.

Rahotanni sun ce maharan sun yi ta harbe-harbe, lamarin da ya tilasta wa mazauna neman taimakon jami’an tsaro cikin gaggawa.

Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya yi zargin cewa maharan sun dasa bam a hanyar Isa zuwa Bargaja.

Turji ya sake fitar da sabon bidiyo a Sokoto
Daya daga cikin jagororin yan ta'adda, Bello Turji. Hoto: @zagazOlamakama.
Source: Facebook

Sabon bidiyon da Bello Turji ya sake

A cikin bidiyon da aka danganta da Turji, shugaban ‘yan bindigar ya bayyana farin cikinsa kan mutuwar wasu da ya kira maƙiyansa.

Bello Turji ya yi ikirarin cewa Allah ya ba su nasara a kan waɗanda yake zargin suna kwace dabbobinsu tare da kashe mutanensu.

Kara karanta wannan

Ana zargin mayakan Turji suna karbar horaswar manya da sababbin makamai

Ya ce:

“Mun gode wa Allah da Ya ba mu damar ganin wannan ranar Asabar, 20 ga Yuni. Bayan godiya ga Allah, a wannan ƙasarmu ta Najeriya, musamman a wasu yankunan da muka dade muna fuskantar ƙalubale.
“In sha Allahu, Allah Ya ba mu nasara a kan waɗanda suke satar dabbobinmu tare da kashe ‘yan’uwanmu marasa laifi a wasu ƙananan hukumomi da suka haɗa da Isa, Zamfara, Sokoto da Sabon Birni da sauran yankunan da ke kewaye.
“Allah Ya ba mu nasara a kan waɗannan mutanen da suke kai hare-hare a kanmu tare da kwace mana dabbobinmu. Mun yi nasarar kashe wasu daga cikinsu, sannan mun ƙwato dabbobinmu daga hannunsu.”

Sai dai ba a samu wata hanya mai zaman kanta da ta tabbatar da sahihancin waɗannan ikirarai da ke cikin bidiyon ba.

Ana zargin yaran Turji na karbar horo

An ji cewa wasu majiyoyi sun fara zargin cewa mayaƙan da ke biyayya ga rikakken dan ta'adda, Bello Turji na samun horo.

Kara karanta wannan

Bayan kisan Rabe, an yaɗa cewa an kashe babban kwamanda, sojoji sun yi martani

An ce wasu manyan na hannun damansa suna jagorantar atisayen soja tare da sababbin mayaƙa da makamai masu ƙarfi.

Wata kungiya ta buƙaci hukumomi su ƙara sa ido tare da binciken bayanan domin dakile duk wata barazana ga rayuka da dukiyoyi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.