Bidiyon ragargaza sansanin 'Major' da soji suka yi a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja
- Rundunar dakarun soji karkashin Operation Thunder Strike sun ragargaji 'yan bindiga a Kaduna
- Bayan bayanan sirrin da rundunar ta samu, ta je ta jiragen yaki har sansanin wani gagararren dan bindiga mai suna Major
- Tare da taimakon sojin kasa ne suka zagaye yankin Kuku da ke karamar hukumar Kagarko inda suka lallasa wa 'yan bindigar wuta
Rundunar sojin kasa tare da na sama karkashin Operation Thunder Strike sun halaka 'yan bindiga masu tarin yawa a wani sansaninsu da ke Kuku a karamar hukumar Kagarko a kan babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja.
Lamarin ya faru ne a ranar Talata, 17 ga watan Nuwamban 2020 bayan bayanan sirrin da dakarun suka samu na sansanin 'yan bindigan da ke hanyar karkashin shugabancin wani gagararre mai suna Major.
Dakarun sun fara ne ta hanyar tura jiragen yaki na sojin saman Najeriya har guda 6 inda suka fara da gano sansanin kafin su fara aman wuta.
Kashi na biyu shine lokacin da dakarun suka je da jiragen sama masu bindiga tare da taimakon sojin kasa da suka shiga ta Kagarko suka zagaye sansanin.
Hakan ya bai wa dakarun damar tarwatsa sansanin tare da kashe 'yan bindigar ba tare da sun tsere ba.
KU KARANTA: Kyawawan hotunan tagwaye maza za su aura tagwàye sun janyo cece-kuce
KU KARANTA: Bayan komawar Umahi APC, ga jerin gwamnonin PDP da za su biyo shi, Uzodinma
A wani labari na daban, rundunar sojin sama ta Operation LAFIYA DOLE, ta ragargaji 'yan Boko Haram a dajin Sambisa da ke jihar Borno, jaridar Leadership ta wallafa.
Kakakin rundunar sojin, Manjo Janar John Enenche, ya ce rundunar ta yi harbin ne ta sama, a bangarori 2, bangaren Sambisa da Gobara, inda yace sun yi amfani da salo na musamman don kai wa 'yan Boko Haram din hari.
Ya ce sojojin sun yi harbin ne daidai wuraren da suke zargi. Saboda sai da suka duba kuma suka yi nazari a wuraren da 'yan ta'addan suka kafa daba, tukunna suka yi harbin. Hakan ya yi sanadiyyar kashe yawancinsu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng