ASUU ta musanta komawa aiki, ta sanar da ranar cigaba da tattaunawa da FG

ASUU ta musanta komawa aiki, ta sanar da ranar cigaba da tattaunawa da FG

- A jiya ne labarai suka fara yawo a kan janye yajin aikin watanni 8 na ASUU

- Kungiyar ta fito fili ta musanta labaran, inda ta wallafa cewa labarin na bogi ne

- A cewar kungiyar gwamnatin tarayya dai ta bukaci yin wani taro dasu ranar Juma'a

ASUU ta musanta janye yajin aikin da ta tafi tun watanni 8 da suka gabata.

Wannan al'amarin yazo ne bayan bayyanar wata takarda, wacce tayi ta yawo a kafafen sada zumuntar zamani, mai tabbatar da janye yajin aikin kungiyar.

ASUU ta wallafa hotunan takardar, inda tace kada mutane su aminta da labarin, na bogi ne.

Kamar yadda ta wallafa, "Gwamnatin tarayya ta ce za ta yi wani taro da ASUU ranar Juma'a.

"Ma'aikatar kwadago da ayyuka ta bayyana hakan ranar Laraba da daddare.

"Ana sa ran za a tattauna a kan wani tsari na biyan malamai albashi, wanda kungiyar ta gabatar da kuma sauran matsaloli da suka shafi kungiyar."

KU KARANTA: Buhari ya so daukar mace daga yankin Ibo a matsayin mataimakiyarsa a 2015, Fadar shugaban kasa

ASUU ta musanta komawa aiki, ta sanar da ranar cigaba da tattaunawa da FG
ASUU ta musanta komawa aiki, ta sanar da ranar cigaba da tattaunawa da FG. Hoto daga @ASUUNGR
Asali: Twitter

KU KARANTA: Bidiyon ragargaza sansanin 'Major' da soji suka yi a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja

A wani labari na daban, Sifeta janar na 'yan sanda, Mohammed Adamu, ya ce babbar matsalar da jami'an tsaro suke fuskanta wurin yin aiki shine yadda 'yan Najeriya suka yanke tsammani daga su.

A cewarsa, gabatar da 'yan sandan unguwanni yana daya daga cikin hanyoyin dawo da yardar mutane a garesu, The Nation ta wallafa.

Adamu, wanda ya samu wakilcin DIG na 'yan sanda, Olushola Oyebande, ya ce yanzu haka ana kokarin yin gyare-gyare don dawo da yardar al'umma a garesu, a wata tattaunawa da 'yan majalisar wakilai.

A cewarsa: "Mun san cewa 'yan sanda suna da damar rayuwa da kuma magana kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanadar. Suna da damar tsare kansu daga 'yan ta'adda da makamansu."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel