Zaben 2027: Tikitin Takarar Atiku Abubakar da Amaechi Ya Fara Tayar da Kura a Jam'iyyar ADC

Zaben 2027: Tikitin Takarar Atiku Abubakar da Amaechi Ya Fara Tayar da Kura a Jam'iyyar ADC

  • Rikici na neman kunno kai a ADC bayan ayyana Rotimi Amaechi a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa a zaben 2027
  • Wasu magoya bayan dan takarar shugaban kasa, Atiku Abhbakar na adawa da zaben Amaechi tare da neman a sauya shi
  • Bangaren Atiku ya ce jinkirin kaddamar da Amaechi ya samo asali ne daga tafiyar da tsohon mataimakin shugaban kasar ya yi zuwa kasashen waje

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Jam’iyyar ADC na fuskantar barazanar barkewar sabon rikici kasa da mako guda bayan ayyana tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa

Idan baku manta ba dan takarar shugaban kasa na ADC, Atiku Abubakar, ya sanar da Rotimi Amaechi a matsayin abokin takararsa yayin da ake tunkarar babban zaben 2027.

Kara karanta wannan

'Da man fetur ya kai N10,000': Sarki ya fadi yadda Dangote ya ceci Najeriya

Atiku da Amaechi.
Dan takarar shugaban kasa na ADC, Atiku Abubakar da abokin takararsa, Rotimi Amaechi Hoto: @Atiku
Source: Twitter

Rikici ya kunno kai a ADC

Jaridar Guardian ta rahoto cewa wasu jiga-jigan jam’iyyar ADC masu biyayya ga Atiku da kuma magoya bayan Amaechi sun fara samun sabani kan batun tikitin mataimakin shugaban kasa.

Rahotanni sun nuna cewa wasu daga cikin magoya bayan tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku na neman a maye gurbin Amaechi.

Dalilin jinkirin kaddamar da Amaechi

Sai dai bangaren Atiku ya bayyana cewa jinkirin kaddamar da Amaechi a hukumance ba ya da alaka da rikici, yana mai cewa Atiku ya yi wata gajeruwar tafiya ta kasuwanci zuwa kasashen waje.

Rahoton This Day ya nuna cewa hadimin yada labaran Atiku, Abdulrasheed Shehu, ya bayyana cewa komai yana tafiya yadda ya kamata tsakanin Atiku da Amaechi.

Ya ce:

“Atiku da Amaechi sun cimma matsaya. Mai girma Atiku ya yi wata gajeruwar tafiya ta kasuwanci. Da zarar ya dawo, za a kaddamar da Amaechi a hukumance cikin kwanaki masu zuwa.”

Kara karanta wannan

Wasu mutanen Zamfara za su baro wa ministan tsaro aiki kan zargin badakalar takardu

Magoya bayan Atiku sun fara bore

Wasu na kusa da Atiku ba su gamsu da zaben Amaechi ba, suna zargin cewa tsofaffin jiga-jigan gwamnatin Muhammadu Buhari ne suka mara masa baya domin samun wannan matsayi.

Haka kuma, wasu daga cikin magoya bayan Atiku sun bayyana cewa Amaechi mutum ne mai zaman kansa wanda zai iya hana su samun tasiri a cikin tsarin yakin neman zabe da kuma gwamnatin da za a kafa idan jam’iyyar ta yi nasara.

Atiku.
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar a taron ADC Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

A wani bangare kuma, jigon ADC a jihar Katsina, Mustapha Inuwa, ya nuna damuwa kan yadda jam’iyyar ke tafiyar da harkokinta.

Inuwa ya bayyana cewa rashin warware matsalolin da suka biyo bayan zabukan fidda gwani ya sa wasu magoya baya suka fara rasa kwarin gwiwa a kan jam’iyyar.

“Jam’iyyar da mutane suka sa rai da fata a kanta ita ce t fara tafiya da irin wannan rikici. Wannan abin takaici ne sosai," in ji shi.

Kara karanta wannan

Tuna baya: Yadda Amaechi ya yi fatali da batun zama dan takarar mataimakin shugaban kasa a ADC

Yadda Amaechi ya cika baki a baya

A wani rahoton, kun ji cewa Rotimi Amaechi ya taba yin watsi da batun yiwuwar zama dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar ADC a baya kafin zaben fitar da gwani.

A wat tattaunawa da aka yi da shi a watan Mayun 2026, tsohon ministan har hasala ya yi da aka yi masa tambayar ko zai iya zama dan takarar mataimakin shugaban kasa na ADC.

Kusan mako guda bayan haka, Alhaji Atiku Abubakar ya lashe tikitin takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC mai adawa kuma ya dauki Amaechi a matsayin abokin takara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262