EndSARS: Na kwashe wata 7 a gidan yari a kan tambayar dan sanda kudin mota, Direban Tasi

EndSARS: Na kwashe wata 7 a gidan yari a kan tambayar dan sanda kudin mota, Direban Tasi

- Wani direban tasi ya bayyana cutarwar da 'yan sanda suka yi masa har yayi watanni 7 a gidan gyaran hali

- A cewarsa, sun shiga motarsa, suka ki biyansa kudin mota, daga ya bukaci hakkinsa sai suka kulla masa tuggu da makirci

- 'Yan sandan sun hadashi da wasu masu fasa bututun man fetur, inda kotu ta yanke musu hukunci tare

Wani direban tasi a jihar Ogun, Mayowa Ayodele, ya bayyana yadda 'yan sanda suka adana shi a gidan gyaran hali na tsawon watanni 7, saboda ya bukaci su biya shi kudin mota.

Ayodele, ya bayyana yadda ya fuskanci cin zarafi da cutarwar a hannun 'yan sanda a Abeokuta, ranar Laraba.

A cewarsa, 'yan sanda 4 suka yi shatar motarsa a ranar 7 ga watan Maris, 2018, amma suka ki biyanshi, Premium Times ta wallafa.

Bayan ya bukaci su biya shi hakkinsa suka kulla masa sharrin da yayi sanadiyyar daure shi a gidan gyaran hali.

A cewarsa, cikin 'yan sanda da suka cutar da shi sun hada da Buhari Yusuf, Ehimere Anthony da wasu 2 da ba zai iya tuna sunayensu ba.

Kamar yadda yayi bayani, "Na dauke su tun daga Mowe zuwa Magboro, na kuma mayar da su Shagamu. Bayan na ajiye su, sai na bukaci su biyani hakkina, N4500, amma suka ki.

"Suka ce ai gwamnati suke yi wa aiki. Bayan na matsa, sai suka ce wa shugabansu ya daure ni, na fasa bututun man fetur."

Kamar yadda Ayodele yace, an kulleshi a Motor Traffic Division da ke Shagamu. Sai da yayi kwana 16 kafin a kai shi babbar kotu da ke Oke Mosan da ke Abeokuta inda aka yanke masa hukuncin fasa bututun man fetur.

Daga nan aka wuce dashi gidan gyaran hali dake Oba, inda yayi watanni 7.

KU KARANTA: IGP: 'Yan Najeriya sun sare, basu yadda da mu ba

EndSARS: Na kwashe wata 7 a gidan yari a kan tambayar dan sanda kudin mota, Direban Tasi
EndSARS: Na kwashe wata 7 a gidan yari a kan tambayar dan sanda kudin mota, Direban Tasi. Hoto daga @Premiumtimes
Asali: Twitter

KU KARANTA: An fasa kotun da ake zaman shari'ar Sarkin Zazzau tare da tarwatsa ofishin alkali

A wani labari na daban, Sanatan daga jihar Abia, Enyinnaya Abaribe, ya jajirce a kan mulkin dan kabilar Ibo a shekarar 2023.

Ya fadi hakan ne a ranar Laraba, 18 ga watan Nuwamba, lokacin da kungiyar manema labarai na Najeriya, NUJ a jihar Imo suka gayyace shi don bashi jinjina ta musamman a matsayinsa na "Sanatan kudu maso gabas da yafi kowa kwazo a 2020."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel