IGP: 'Yan Najeriya sun sare, basu yadda da mu ba
- Babbar matsalar da 'yan sanda suke fuskanta shine rashin jituwa tsakaninsu da mutane, cewar Sifeta janar na 'yan sanda
- A cewar Mohammed Adamu, mutane da dama suna nuna rashin yarda tsakaninsu da 'yan sanda, kuma hakan yana kawo matsaloli
- A cewarsa, ana son a magance hakan ne ta hanyar samar da 'yan sandan anguwanni, ana fatan hakan zai kawo maslaha
Sifeta janar na 'yan sanda, Mohammed Adamu, ya ce babbar matsalar da jami'an tsaro suke fuskanta wurin yin aiki shine yadda 'yan Najeriya suka yanke tsammani daga su.
A cewarsa, gabatar da 'yan sandan unguwanni yana daya daga cikin hanyoyin dawo da yardar mutane a garesu, The Nation ta wallafa.
Adamu, wanda ya samu wakilcin DIG na 'yan sanda, Olushola Oyebande, ya ce yanzu haka ana kokarin yin gyare-gyare don dawo da yardar al'umma a garesu, a wata tattaunawa da 'yan majalisar wakilai.
A cewarsa: "Mun san cewa 'yan sanda suna da damar rayuwa da kuma magana kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanadar. Suna da damar tsare kansu daga 'yan ta'adda da makamansu.
"Amma duk da haka, bamu basu damar yin hakan ba, don gudun kashe-kashe su yawaita a al'umma.
"Yanzu haka, akwai hanyoyi iri-iri da yanzu haka suke horar da 'yan sanda, don mutane su kara yarda da su.
"Yanzu babbar matsalarmu ita ce rashin jituwa, tsakanin mutane da 'yan sanda.
"Shiyasa gwamnatin yanzu ta tsaya tsayin-daka don ganin an yi gyara a kan wannan matsalar, ta hanyar samar da 'yan sandan anguwanni."
KU KARANTA: Bayan komawar Umahi APC, ga jerin gwamnonin PDP da za su biyo shi, Uzodinma
KU KARANTA: Na dinga hailala da istigfari a yayin da nake killace sakamakon korona, Gwamnan Niger
A wani labari na daban, fadar shugaban kasa ta musanta zargin da yake ta yawo a kan cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya tsani 'yan kabilar Ibo kuma bai yarda da bai wa mata dama ba a harkar mulki.
A ranar Talata, 17 ga watan Nuwamba, Bashir Ahmad, hadimin shugaban kasa a harkar labarai, ya musanta zargin da ake yi wa shugaban kasan.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng