2023: Ministocin Buhari 2 suna zawarcin kujerarsa

2023: Ministocin Buhari 2 suna zawarcin kujerarsa

- Bayani da zafi ya nuna cewa wasu ministocin Buhari biyu suna zawarcin kujerarsa

- Kamar yadda aka gano, suna daga cikin wadanda suka assasa sauke Adam Oshiomhole

- An gane cewa basu son tsarin mulkin karba-karba na jam'iyyar APC yayi tasiri a 2023

Duk da jan kunnen da aka yi na gujewa jan hankalin shugaban kasa Muhammadu Buhari yayin mulkinsa, biyu daga cikin ministocinsa na zawarcin kujerarsa a shekarar 2023 mai zuwa.

Minsitocin da lamarin ya shafa su ake zargi da assasa tsige tsohon shugaban jam'iyyar APC, Adams Oshiomhole.

Hakazalika, a halin yanzu suna ta neman mafita domin samun cikar burinsu a karkashin jam,'iyyar APC din, jaridar The Nation ta wallafa.

Sun ja tunga sun tsaya tare da jan layi inda basu so a bada damar mulkin karba-karba na yanki da jam'iyyar APC ke so.

Tunda abin da a halin yanzu suka hararowa shine yadda za su haye kujerar mulkin kasar nan, sun nuna rashin amincewarsu na mulkin karba-karba.

Lokaci kadai ake jira inda ministocin biyu za su bayyana kansu.

KU KARANTA: Kashe-kashe da garkuwa da mutane: Fasinjoji sun kauracewa hanyar Kaduna zuwa Abuja

2023: Ministocin Buhari 2 suna zawarcin kujerarsa
2023: Ministocin Buhari 2 suna zawarcin kujerarsa. Hoto daga @Thenation
Asali: Twitter

KU KARANTA: IGP: 'Yan Najeriya sun sare, basu yadda da mu ba

A wani labari na daban, Zainab Buba galadima, diyar makusancin shugaban kasa Muhammadu Buhari a da, Buba Galadima, ta ce har a halin yanzu mahaifinta dan jam'iyyar APC ne.

Kamar yadda Zainab, wacce tsohuwar jami'a ce a fadar shugaban kasa, ta ce akwai bukatar gyara a gwamnatin Buhari a irin abubuwan da ta gani.

Ta ce in dai aiki a fadar ne, toh a kai kasuwa. "Na dandana kuda ta saboda gani-gani da wasu suka dinga min yayin da nake aiki a fadar shugaban kasan. Akwai masu min bakar magana, babu wanda ban gani ba," ta ce saboda sabanin mahaifinta da Buhari."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel