Buhari ya so daukar mace daga yankin Ibo a matsayin mataimakiyarsa a 2015, Fadar shugaban kasa
- Fadar shugaban kasa ta ce duk masu yi wa shugaba Buhari bakin fenti, su sauya wani salon saboda ba hakan bane
- Akwai masu yada labaran bogi, suna cewa ya tsani 'yan kabilar Ibo, Buhari ya tsani bai wa mata damar shugabanci
- Hadimin shugaban kasa, Ahmad, ya ce Buhari ya bukaci mace kuma 'yar kabilar Ibo ta tsaya a mataimakiyarsa a 2011, amma ta ki
Fadar shugaban kasa ta musanta zargin da yake ta yawo a kan cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya tsani 'yan kabilar Ibo kuma bai yarda da bai wa mata dama ba a harkar mulki.
A ranar Talata, 17 ga watan Nuwamba, Bashir Ahmad, hadimin shugaban kasa a harkar labarai, ya musanta zargin da ake yi wa shugaban kasan.
Ya wallafa a shafinsa na kafar sada zumuntar zamani ta Twitter, inda yace, "Shugaban kasa bai tsani 'yan kabilar Ibo ba. Sannan duk masu yada wannan maganar, su canja salo."
Ahmad ya kara bayani a kan yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya zabi Ibo a matsayin mataimakiyarsa, lokacin da ya tsaya takarar shugabancin kasa a 2011.
Ya kara bayani a kan yadda shugaban kasar ya so tsayar da mace a matsayin mataimakiyarsa amma ta ki amincewa.
A cewarsa, "Duk wadanda suke yi wa shugaban kasa bakin fenti, suna yi masa kage, cewa bayason Ibo kuma bai amince da bai wa mace damar shugabanci ba, su canja salo.
"Idan ba a manta ba, 2011, lokacin da shugaban kasa ya tsaya takara a karkashin jam'iyyar CPC, ya nemi 'yar kabilar Ibo, kuma mace, ta tsaya a matsayin mataimakiyarsa, amma ta ki amincewa."
KU KARANTA: Hotunan auren dole da aka yi wa yarinya mai shekaru 13 da dattijo mai shekaru 48
KU KARANTA: Dakarun sojin saman Najeriya sun ragargaza sansanin 'yan Boko Haram a Sambisa
A wani labari na daban, Gwamna Hope Uzodinma ya ce bayan David Umahi ya koma jam'iyyar APC, gwamnoni da dama za su yi ta tururuwar shiga jam'iyyar.
Gwamnan jihar Imo ya fadi hakan ne a wata takarda ta ranar Litinin, 16 ga watan Nuwamba, bayan ya ziyarci babban ofishin APC da yake Abuja, kamar yadda The Nation ta ruwaito.
Uzodinma ya ce kwanan nan gwamnoni PDP za su yi ta komawa APC.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng