Bayan Kalaman Trump, Firayim Ministan Birtaniya Ya Sauka daga Mukaminsa

Bayan Kalaman Trump, Firayim Ministan Birtaniya Ya Sauka daga Mukaminsa

  • Firayim Ministan Birtaniya, Sir Keir Starmer, ya sanar da murabus daga mukaminsa bayan ya shafe ƙasa da shekaru biyu a kan mulki
  • Starmer ya bayyana cewa za a fara zaben sabon shugaban Jam’iyyar Labour a watan Yuli, yayin zai ci gaba da rike mukamin Firayim Minista
  • Murabus ɗin ya biyo bayan watanni na rikice-rikicen siyasa, sauyin manufofi, raguwar farin jini a wajen jama’a, da kalaman Donald Trump

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Birtaniya - Firayim Ministan Birtaniya, Keir Starmer, ya sanar da yin murabus daga mukaminsa a ranar Litinin, lamarin da ya kawo karshe wa’adinsa da bai kai shekaru biyu ba a ofis.

A jawabi mai cike da sosa rai da ya yi a wajen gidan gwamnati na 10 Downing Street, Starmer ya ce ya dauki dukkan matakai a gwamnatinsa don kare muradun kasar da yake kauna.

Kara karanta wannan

"Firaministan Birtaniya zai yi murabus," Donald Trump ya yi magana kan Keir Starmer

Firayim Ministan Birtaniya, Sir Keir Starmer ya yi murabus daga mukaminsa
Firaministan Birtaniya, Keir Starmer yana magana a London a ranar 28 ga Fabrairu, 2026 bayan Amurka da ISra'ila sun farmaki Iran. Hoto: Jonathan Brady / POOL / AFP via Getty Images
Source: Getty Images

Firayam Ministan Birtaniya ya yi murabus

Kafar watsa labarai ta BBC ta rahoto Firayam Ministan yana bada tabbacin cewa cewa zai sauka daga shugabancin Jam’iyyar Labour.

Starmer ya bayyana cewa Jam’iyyar Labour za ta fara tsarin zaben sabon shugabanta a watan Yuli, inda ya ce zai ci gaba da rike mukamin Firayim Minista har sai an kammala zaben wanda zai gaje shi.

Ya kara da cewa zai yi duk mai yiwuwa domin tabbatar da mika mulki cikin lumana da tsari kafin majalisar dokoki ta dawo daga hutun bazara a watan Satumba.

Murabus din Starmer ya biyo bayan watanni na matsin lamba daga cikin jam’iyya da kuma suka daga jama’a kan yadda gwamnatinsa ke tafiyar da harkokin kasa.

Sababbin sauye-sauyen siyasa a Birtaniya

A lokacin mulkinsa, an samu sauyin manufofi da dama, murabus din manyan jami’an gwamnati, da kuma karuwar rashin jituwa kan batutuwan tattalin arziki da tsaro.

Kara karanta wannan

Abin tausayi: Ɗan kasuwa ya mutu a wani yanayi a ɗakin fitacciyar 'yar TikTok a jihar Kano

Hankali ya karkata ga tsohon minista Andy Burnham, wanda ake ganin zai taka muhimmiyar rawa a takarar shugabancin Labour bayan nasarar da ya samu a wani zabe na musamman da ya ba shi damar komawa majalisa.

Wannan na nuna yadda jam’iyyar Labour ke shiga sabon salo na fafatawar shugabanci bayan murabus din Starmer.

Firayim Ministan Birtaniya ya yi murabus bayan fuskantar matsin lambar siyasa.
Firaministan Birtaniya, Keir Starmer yana magana da 'yan jarida bayan taron G7. Hoto: Isabel Infantes - WPA Pool/Getty Images
Source: Getty Images

Tarihin da Starmer ya kafa a Birtaniya

Duk da murabus din, Starmer ya taba samun yabo a baya saboda rawar da ya taka wajen mayar da Jam’iyyar Labour mai karfi, wadda ta lashe babban zabe a 2024 tare da kawo karshen mulkin Conservative na tsawon shekaru 14.

Sai dai wa’adinsa ya gamu da kalubale da dama, ciki har da cece-kuce kan wasu manufofi da kuma karuwar tasirin sababbin kungiyoyin siyasa masu adawa, in ji rahoton CNN.

A jawabin bankwana, Starmer ya bayyana fatan cewa wanda zai gaje shi zai ci gaba da gina Birtaniya mai karfi da adalci, tare da tabbatar da goyon bayansa ga mika mulki cikin lumana.

'Starmer zai yi murabus' - Donald Trump

Tun da fari, mun ruwaito cewa, Donald Trump ya ce Firaministan Birtaniya Keir Starmer zai yi murabus saboda gazawa kan batutuwan shige da fice da makamashi.

Kara karanta wannan

"Mijina yana kawo ƴan mata ya kwanta da su a gadon aurenmu," Mata ta fada wa Kotu

Shugaban Amurka ya soki manufofin Firaminista Starmer, yayin da ake samun rade-radin matsin lamba daga wasu ‘yan jam’iyyar Labour.

Rahotanni sun ce wasu ministoci na matsa wa Starmer lamba ya tsara lokacin mika mulki bayan rikicin cikin gida da ya dabaibaye London.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com