Na ga tsabar wulakanci yayin da nake aiki a fadar Buhari, Diyar Buba Galadima

Na ga tsabar wulakanci yayin da nake aiki a fadar Buhari, Diyar Buba Galadima

- Diyar tsohon makusancin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Buba Galadima, ta koka da gwamnatin Buhari

- Ta bayyana yadda ta yi aiki na tsawon lokaci a fadar shugaban kasan amma ba a taba biyanta ba kuma ga wulakanci da take fuskanta

- Zainab ta ce a wani bangare kuma jama'a suna kallon cewa ana gwangwajeta ne da ababen arziki a rayuwa

Zainab Buba galadima, diyar makusancin shugaban kasa Muhammadu Buhari a da, Buba Galadima, ta ce har a halin yanzu mahaifinta dan jam'iyyar APC ne.

Kamar yadda Zainab, wacce tsohuwar jami'a ce a fadar shugaban kasa, ta ce akwai bukatar gyara a gwamnatin Buhari a irin abubuwan da ta gani. Ta ce in dai aiki a fadar ne, toh a kai kasuwa.

"Na dandana kuda ta saboda gani-gani da wasu suka dinga min yayin da nake aiki a fadar shugaban kasan. Akwai masu min bakar magana, babu wanda ban gani ba," ta ce saboda sabanin mahaifinta da Buhari.

A wata hira da Aminiya Daily Trust ta yi da diyar Buban, ta ce shakarunta hudu tana aiki a fadar shugaban kasan amma ba a biyanta albashi. Duk yadda ta so a bata hakkinta, ya gagara.

Zainab wacce Buhari ne madaurin aurenta, ta ce, "A gaskiya ni ban yi aiki a ofishin mataimakin shugaban kasa ba don a biya ni."

"Na yi kokari mai yawa amma mutanen da ke kusa da Buhari kullum ba su gani. Daga nan ne na hakura kawai da aikin."

"A wani bangare kuma ana nuna cewa gwanati ta rungumeni ana min sha tara ta arziki, amma ba hakan bane." tace.

KU KARANTA: Kashe-kashe da garkuwa da mutane: Fasinjoji sun kauracewa hanyar Kaduna zuwa Abuja

Na ga tsabar wulakanci yayin da nake aiki a fadar Buhari, Diyar Buba Galadima
Na ga tsabar wulakanci yayin da nake aiki a fadar Buhari, Diyar Buba Galadima. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: An fasa kotun da ake zaman shari'ar Sarkin Zazzau tare da tarwatsa ofishin alkali

A wani labari na daban, Sanatan daga jihar Abia, Enyinnaya Abaribe, ya jajirce a kan mulkin dan kabilar Ibo a shekarar 2023.

Ya fadi hakan ne a ranar Laraba, 18 ga watan Nuwamba, lokacin da kungiyar manema labarai na Najeriya, NUJ a jihar Imo suka gayyace shi don bashi jinjina ta musamman a matsayinsa na "Sanatan kudu maso gabas da yafi kowa kwazo a 2020."

Abaribe, wanda yake wakiltar Abia ta kudu, ya lashi takobin kare hakkin yankinsa, don tabbatar musu da adalci.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel