Sowore: Kotu Ta Bada Umarnin Tsare Dan Takarar Shugaban Kasa a Gidan Yarin Kuje
- Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta tura Omoyele Sowore zuwa gidan yarin Kuje bayan ta dakatar da bukatar soke umarnin belinsa na baya
- Hukumar DSS na tuhumar Sowore da wallafa kalaman karya kan Shugaba Bola Tinubu a shafukan sada zumunta na X da Facebook
- A yayin zaman kotun, Mai shari’a Muhammad Umar ya ki amincewa da bukatar cire kansa daga shari’ar, ya kuma dage sauraron karar zuwa jibi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Wata Babbar Kotun Tarayya da ke zaune a Abuja ta bada umarnin tsare dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar AAC, Omoyele Sowore, a gidan gyaran hali na Kuje.
Sowore zai ci gaba da kasancewa a tsare har sai kotu ta saurari bukatar da sababbin lauyoyinsa suka shigar, wadda ke neman a soke umarnin da ya soke belinsa.

Source: Facebook
Kotu ta bada umarnin tsare Yele Sowore
A zaman da ya gabata, Sowore bai halarci kotu ba, lamarin da ya sa masu gabatar da kara suka roki kotu da ta soke belinsa, suna zargin cewa yana amfani da dabarun jinkirta shari’a, in ji rahoton TVC News.
Ko da yake Sowore ya aike wa kotu wasika a zaman da ya gabata yana neman a dage shari’ar, bai bayyana dalilin rashin zuwansa ba.
A zaman da aka gudanar a yau Litinin, Sowore ya halarci kotu tare da lauyansa, Olumide Fusika, wanda babban lauyan Najeriya (SAN) ne.
Mai shari’a Muhammad Umar ya yanke hukunci cikin gaggawa inda ya umarci a tsare Sowore a gidan gyaran hali har sai an saurari kuma an yanke hukunci kan bukatarsa ta soke umarnin da ya soke belinsa da kuma sammacin kama shi.
Shari'ar Sowore kan batanci ga Tinubu
Alkalin ya kuma yi watsi da bukatar Sowore ta neman ya janye daga shari’ar saboda zargin nuna son kai.
An daga sauraron shari’ar zuwa ranar 24 ga watan Yuni domin ci gaba da sauraron bukatar, in ji rahoton Vanguard.
Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ce ke tuhumar Sowore kan zargin wallafa kalaman karya kan Shugaba Bola Ahmed Tinubu a shafukansa na X da Facebook.

Source: Getty Images
Martanin Sowore kan umarnin tsare shi
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, Sowore ya yi martani kan wannan umarni, yana mai cewa:
"Mai shari'a M.G Umar na babbar kotun tarayya a Abuja ya bada umarnin a tsare ni a gidan yarin Kuje saboda ban halarci zaman kotu sau daya ba, tun bayan fara wannan shari'ar ta bita da kulli, duk da lauyoyina sun sanar da kotu dalilin rashin halarta ta.
" Ni wannan bai dame ni ba ko kadan. Daure mutum a gidan yari bai taba zama nasara kan gaskiya ba. Ina kira ga 'yan Najeriya da masu kishin kasar da kada su raunana, kada su mika wuya, kada su gajiya a kokarin da muke yi na kwato Najeriya daga masu mulkin kama karya."
- Omoyele Sowore.
Karanta sakon a nan kasa:
Shirin Sowore idan ya ci zaben 2027
A wani labari, mun ruwaito cewa, Omoyele Sowore, ya bayyana yadda zai shawo kan matsalar tsaron Najeriya da ya ce ya yi kamari idan ya ci zaben 2027.
Sowore, dan takarar AAC, ya yi alƙawarin amfani da jirage marasa matuka a matsayin Ministan Tsaro idan ya zama shugaban Najeriya a 2027.
Ya ce zai kafa wata cibiyar kula da tsaro wadda za ta rika bin diddigin ‘yan ta’adda tare da dakile su cikin gaggawa ta hanyar amfani da fasahar zamani.
Asali: Legit.ng


