Muneerat Abdulsalam ta samu tallafi daga wata kungiya, za ta ga likitan kwakwalwa

Muneerat Abdulsalam ta samu tallafi daga wata kungiya, za ta ga likitan kwakwalwa

- Malamar mata, Munirat Abdulsalam, ta samu tallafi daga kungiyar mata Women in Da'awah

- Ta bayyana cewa, kungiyar ta bata naira dubu talatin domin karfafa kasuwancinta da kuma ganin likitan kwakwalwa

- Ta yi kira ga jama'a da su kiyayi hantara tare da cin zarafin fitattun jama'a a kafafen sada zumunta

Fitacciyar malamar mata, mai bayani a kan zamantakewar aure, Munirat Abdulsalam ta samu tallafi daga kungiyar Women in Da'awa.

Kamar yadda Legit.ng ta samu tattaunawa da ita, ta bayyana cewa kungiyar ta shiga matsananciyar damuwa a kan lamarin da ya faru a makonni kadan da suka gabata.

Idan za mu tuna, Munirat Abdulsalam ta wallafa wani bidiyo inda ta sanar da ficewarta daga addinin Musulunci sakamakon tsangwama, barazana ga rayuwa da sauran hantara da take fuskanta daga jama'a.

Muneerat Abdulsalam ta samu tallafi daga wata kungiya, za ta ga likitan kwakwalwa
Muneerat Abdulsalam ta samu tallafi daga wata kungiya, za ta ga likitan kwakwalwa. Hoto daga en.videos2be.com
Asali: Getty Images

Malamar matan, ta ce suna cikin sahun gaba da suka fara tuntubarta tare da son sanin damuwarta tun bayan aukuwar lamarin.

A ranar Juma'a da ta gabata, Munirat ta wallafa wani hoto da ke nuna shigar kudi har naira dubu talatin asusun bankinta tare da sakon godiya ga kungiyar.

A yayin da Legit.ng ta tuntubeta, ta tabbatar da cewa kungiyar Women in Da'awah ce ta turo mata tare da bukatar ta je ganin likitan kwalkwalwa sannan kuma ta karfafa kasuwancinta.

Munira ta bayyana cewa, ta karba tallafin ne ba don tana cikin mabukata ba, ta karba ne saboda mutunta kungiyar da take yi tare da ganin girman shugabanninta.

KU KARANTA: EndSARS: Na kwashe wata 7 a gidan yari a kan tambayar dan sanda kudin mota, Direban Tasi

Daga bisani, fitacciyar malamar matan ta bukaci jama'a da su dinga bai wa juna uziri tare da tausayawa a rayuwa.

Ta roki jama'a da su kiyayi cin zarafi tare da caccakar jama'a a kafar sada zumuntar zamani.

"Akwai fitattaun jama'a da irin wannan cin zarafin yayi ajali. Ba ku san wanne hali mutum yake a rayuwar shi ba. A dinga bai wa juna uziri tare da tausasawa juna," a cewarta.

Muneerat Abdulsalam ta samu tallafi daga wata kungiya, za ta ga likitan kwakwalwa
Muneerat Abdulsalam ta samu tallafi daga wata kungiya, za ta ga likitan kwakwalwa. Hoto daga Munirat Abdulsalam
Asali: Original

KU KARANTA: Shugabancin kasan yankin Ibo a 2023: Babu gudu, babu ja da baya, Sanata Abaribe

A wani labari na daban, Munirat Abdulsalam, fitacciyar malamar mata kuma mai tattaunawa a kan harkar auratayya, ta bar addinin Musulunci.

Idan za mu tuna, kusan shekaru biyu da suka gabata ne ta dawo addinin Islama inda aka lakana mata kalmar shahada tare da nuna mata wankan komawa addinin Musulunci a babban masallacin kasa da ke Abuja.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel