Albashin ma'aikata
Atiku Abubakar ya bukaci shugaba Bola Tinubu ya kara mafi karancin albashi, yana mai cewa N70,000 ya rasa daraja saboda tsadar man fetur da rayuwa.
Gwamnatin jihar Bauchi ta kori jami’in kashe gobara Abdulkadir Aliyu bayan an same shi da laifin satar takalman jama’a a masallacin sakatariyar da ya ke aiki.
Festus Keyamo ya ce N70,000 ba za ta isa ma’aikata su biya bukatunsu ba, yana kira da a ƙara mafi ƙarancin albashi domin rage matsin tattalin arziki.
Gwamnatin Tarayya ta ce tana shirin sake nazari kan mafi karancin albashin N70,000 a 2027, yayin da kungiyoyin kwadago ke neman kudin ya kai N500,000.
Gwamnan Neja Mohammed Umaru Bago ya ce gonarsa tana biyan wadanda suka kammala jami’a mafi karancin N500k a wata, yayin da ya bukaci karin zuba jari a noma.
Dan takarar AAC, Omoyele Sowore, ya yi alkawarin kafa mafi ƙarancin albashi na N500,000 duk wata da samar da wutar lantarki sa’o’i 24 idan ya ci zaɓen 2027
Sarkin Zazzau, Ahmed Bamalli, ya goyi bayan karin albashin sarakunan gargajiya na Kaduna da kashi 100, yana mai cewa karin zai taimaka wajen rage matsin rayuwa.
Bincike ya gano cewa ma’aikatan tarayya sun nemi ƙarin albashi saboda tsadar rayuwa, ba wai a matsayin sharadin zaɓen jam'iyyar APC a shekarar 2027 ba.
Gwamnatin Singapore ta sanar da ƙarin albashin ministoci da manyan jami’ai, inda Firaminista Lawrence Wong zai samu ƙarin albashi sama da kashi 60%.
Albashin ma'aikata
Samu kari